Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta baiwa al’ummar jihar tabbacin gudanar da sahihin zaben shugabannin kananan hukumomi da za a yi acikin wannan shekarar a jihar.
Shugaban jam’iyyar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayar da wannan tabbacin lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Talata.
- Da Dumi-dumi: Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Tsaro Kan Karuwar Rashin Tsaro
- Ranar Tunawa Da Jarumai: Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da suka Rasu
Dungurawa ya ce “A matsayin jam’iyyarmu ta dimokuradiyya wacce manufofinta suka kasance don muradun jama’a, za mu tabbatar da gudanar da zaben kananan hukumomi cikin ‘yanci da adalci a cikin wannan shekara.”
Ya ce, a wani bangare na tsarin dimokaradiyyar gwamnatin da NNPP ke yi a jihar, shi ne yadda ta baiwa daukacin shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomin jihar damar gudanar da ayyukansu.
Dungurawa, ya godewa al’ummar jihar bisa goyon baya da addu’o’i da suka yi a baya da lokacin da kotun koli ta yanke hukuncin da ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kano.