Zamu Ba ’Yan Nijeriya Mamaki A Gasar Afirka  —Rabiu Ali

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Rabiu Ali wanda akafi sani da Rabiu Pele, ya bayyana cewa zasu bawa magoya bayan kungiyar Super Eagles ta Najeriya mamaki a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta yan wasan cikin gida da ake bugawa a yanzu haka  a kasar Morocco.

Ali, ya bayyana hakane a lokacin da tawagar yan wasan suka tashi daga daukar horo a shirye-shiryen da yan wasan sukeyi na buga wasa da kasar Ekuatorial Guinea.

Yaci gaba da cewa masu horar da yan wasan kungiyar suna yin iya kokarinsu wajen ganin cewa sun samu nasara a wasansu na gaba da zasu buga saboda ana koya musu dabarun yadda zasu zura kwallo a raga.

Ya kara da cewa a kwanakin baya wata kungiya daga kasar Libya ta nemeshi daya buga mata wasa sai dai yarjejeniyarsu bata kammala ba saboda dalilai na kudi.

Yace kungiyar ta kasar Libya, wadda bai ambaci sunanta ba taso yakoma kungiyar sai dai kungiyoyin biyu basu amince da hakan ba sakamakon sunce bazasu biya kungiyar Kano Pillars kudi ba suna son yakoma yaje yayi musu wasa na tsawon watanni hudu a matsayin aro.

A karshe yace yana fatan Kano Pillars zata cigaba da samun nasara a wasannin da suke bugawa na gasar firimiya sannan kuma ya kagu yadawo domin cigaba da fafatawa a kungiyar sakamakon kungiyar tafara gasar da kafar dama.

 

Exit mobile version