Mashawarciya ta musamman kan Harkokin lafiya Dr. Fauziyya Buba Idris ce ta bayyana haka lokacin da ta karbi bakuncin kungiyar cigaban harkokin Kurame ta Jihar Kano KADYAC a ofishinta. Kamar yadda jami’in yada labaran ofishin mashawarciyar ta musamman Auwal Musa Yola ya shaidawa LEADERSHIP A YAU
Tunda farko da yake gabatar da jawabinsa sakataren Kungiyar Kuramen Kwamared Bashir Idris Adamu cewa ya yi sunzo ofishin mashawarciyar ta musamman ne domin neman hadin kanta.
Ya kara da cewa ‘ya’yan kungiyar sun samu shaidar karatu a matakai daban daban a Jihar Kano kuma suna bukatar sa hannun Dr. Fauziyya domin samun nasarorin da suka sa gaba.
Shima da yake gabatar da jawabinsa shugaban Kungiyar Kuramen Kwamared Rabiu Aliyu Adam ya jinjinawa mashawarciyar ta musamman bisa samar da ingantattun hanyoyin ci gaba.