Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ƙaddamar da sabon tsari da zai bayar da tukuici ga baƙin haure da suka shigo ƙasar ta haramtacciyar hanya idan har suka amince su fice daga ƙasar da kansu.
Wannan sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida (DHS) ta kasar ta sanar, na da nufin rage cunkoson da ke barazana ga hukumomin kula da shige da fice. A cewar DHS, “waɗanda suka amince su fice daga kasar domin kashin kansu, za a basu $1,000, kuma, ba za su kasance cikin jerin mutanen da za a kama ko tilasta musu ficewa ba.
- Gwamnan Bauchi Ya Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Banga A Alkaleri
- Saudiyya Ta Tanadi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Yin Aikin Hajji Babu Takardun Izini
“Ficewa daga ƙasar Amurka ba tare da tilastawa ba ita ce hanya me kyau da ta fi dacewa da bakin hauren da suka shigo ba bisa ka’ida ba,” in ji Kristi Noem, Sakataren Tsaron Cikin Gida, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin data gabata.
Trump ya bayyana cewa, waɗanda suka zabi barin ƙasar da kansu na iya samun dama ta hanyar doka don dawowa cikin Amurka nan gaba idan suka cika ka’idojin da suka dace.
A cewar rahoton, an riga an sayo tikitin jirgi ga mutum na farko da ya karɓi wannan tayin — daga birnin Chicago zuwa ƙasar Honduras.
Tun bayan da Trump ya sake komawa kan kujerar mulki a watan Janairu, ya gindaya sabbin matakai masu tsauri don hana baƙin haure shiga ƙasar. Wasu daga cikin waɗannan matakan na haifar da ce-ce-ku-ce, musamman ganin yadda ake amfani da tsofaffin dokokin wanda suke da alaka da zamanin yaƙi wajen aiwatar da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp