Zan Bai Wa Ilimi Da Lafiya Fifiko Idan Na Zama Gwamnan Bauchi, Inji Dakta Dahuwa

A Jiya ne Dakta Sama’ila Dahuwa ya ayyana  bukatarsa na tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a zaben 2019 da ke tafe.

Daktan Dahuwa ya bayyana aniyarsa ne a sakatariyar ‘yan jarida da ke Bauchi a lokacin da ke bayyana muradinsa kan hakan, ya shaida wa manema labarum cewar daga zarar ya samu nasara a zaben da za a fafata nan gaba kadan ilimi da lafiya matsalolinsu za su zama tarihi a Bauchi.

Kachallan Katagum ya bayyana cewar ya fito wannan takarar ne a karkashin jam’iyyar NNPP mai alamar Kwando da kayan dadi, inda ya yi fatan a zabeshi domin maida jihar Bauchi amarya.

Ya ke cewa, jihar Bauchi ta samu kanta a wani mawucin halin da suke da muradin kawo gyara da ci gaba, amma sai an zabesu ne za su iya cimma murafinsu, “Ko yaron da ke goye inda zai iya bude baki ya yi magana zai gaya maka cewar kusan gwamnati bata gudanar da komai a jihar Bauchi. Mu kam a jihar Bauchi muna ganin kamar kason da ake bai wa jihohi daga tarayya bai shigowa cikin Bauchi, domin duk wani abun da ka gani a jihar Bauchi a yau, an yi shi sama da shekaru 20 ko 30 da suka wuce.

“Yanzu idan ka dauki ilimi yadda sha’anin ilimi ya lalace a jihar nan, ka shiga cikin garin Bauchi ba kauyen Bauchi ba za ka tarar da yara 200 a cikin aji babu kuma abun zama, ta yaya ne yaro zai samu ya fahinci abun da ake koyar masa alhali ko nutsuwa bai samu ba.

“Asibiti ne za ka je ka samu ana kwantar da majinyata biyu a gado daya, don haka muna da niyyar idan Allah ya bamu dama za mu zo da tsare-tsare domin kawo sauyi, abun da na ke fada kullum dole ne a kawo sauyi kan wadannan matsalolin,” In ji Dan takarar gwamnan.

Dakta Dahuwa ya ci gaba da shaida cewar kishin jihar da kuma damuwa da halin da jama’an jihar ke ciki ne ya sanya sa tsunduma domin nemar sa’arsa, yana mai bayanin cewar zai yi amfani da kwarewarsa a fagen aiki jinya wajen samar da nagartaccen shugabanci a jihar Bauchi.

Ya ce; “Hakika akwai talauci a Nijeriya, a takaice ma jihar Bauchi tana ta biyu a talauci, alhali a Bauchi ne aka fitar da Firaministan Nijeriya, nan ne garin su Malam Sa’adu Zungur, garin su Farfeso Ibrahim Tahir garin da ta yi irin wannan gagarumin gudunmawa wajen ci gaban kasar nan a ce ta dawo wannan matakin kai ka san shugabancin jihar ta lalace.

“An samu shugabanin da damuwarsu su tara kudi ne da dukiya kawai, mu kuma mun shigo ne ba don mun fi kowa bane, sai don mu yi aiyukan da suka dace domin amfanin ‘ya’yanmu nan gaba,” A cewar shi.

Ya bayyana cewar nagartaccen mutum ne jama’a suke zaba ba wai ‘yan diddiri ba; ya kuma nuna gayar goyon bayansa kan yadda aka bai wa matasa zarafin shigowa cikin harkokin siyasa a dama da su a fadin kasar nan, yana mai bayanin cewar wannan ma babbar nasarace ga jam’iyyarsu ta NNPP, a cewarshi mafiya yawansu matasa ne masu jinni a jika da za su iya kawo sauyi.

Kachallan Katagum wanda dan kasuwa ne a halin yanzu ya shaida cewar bai fito siyasar da gaba ba; inda ya bayyana cewar duk wanda jam’iyyarsu ta amince masa a shirye yake ya mara masa baya domin samun nasarar jam’iyyar a babban zaben da za a fafata a 2019.

 

Exit mobile version