Abba Sadau, ‘ya’yan fitacciyar jaruma Rahama Sadau, ya bayyana alhini kan rasuwar mahaifinsu, Alhaji Ibrahim Sadau, wanda ya kwanta dama a ranar 22 ga watan Yunin da ya gabata, mahaifin nasu dai; ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Talata, kwana daya bayan dawowarsa daga aikin Hajji, ya rasu a asibitin sojoji na 44, da ke Jihar Kaduna da misalin karfe 4:00 na asuba, sanadiyar ciwon Siga.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa, an yi jana’idarsa da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar da ya rasu, a harabar wata makarantar Islamiyya da ke kusa da gidansa, a kan titin Lome da ke Unguwar Rimi.
- INEC Ta Ayyana 16 Ga Agusta Don Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihohi 12
- 2027: Kungiyoyi 110 Ne Ke Neman Rajistan Zama Jam’iyyun Siyasa A Yanzu Haka – INEC
Dattijon mai kimanin shekara 58, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya tara, daga cikinsu akwai jaruma a masana’antar Kannywood, Rahama Sadau; wacce ita ce ‘yarsa ta biyu.
Daya daga cikin ‘ya’yan mamacin, Furodusa Haruna Sadau lbrahim, wanda aka fi sani da Abba Sadau; ya bayyana irin halin kidimewa da ya shiga, sakamakon wancan rashi na mahaifin nasu. Abba, wanda furodusa ne a masana’antar Kannywood, ya ce, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un, wannan rashi ba mu taba yin irinsa ba a danginmu baki-daya, wannan shi ne karo na farko da muka yi irin wannan rashi babba.
“Wannan rashi ya yi matukar taba mu, ya taba kowa da kowa. Domin kuuwa, ni har yanzu ban gama yarda cewa ya mutu ba; bayan dawowarsa daga Saudiyya, ya ce; ba shi da lafiya, daga nan sai ya kira ni a waya ya ce da ni na turo masa likita, sai na ce da shi; kamata ya yi ya je asibiti a duba shi sosai, ana kai shi asibitin, sai labari ya canza; jikin nasa ya yi tsanani sosai”, in ji Abba.
Sadau, ya ci gaba da bayyana yadda zai ci gaba rika tunawa da mahaifin nasu, inda ya ce; “Akwai abubuwa da dama da zan rika tuna mahaifina da su, amma abin da zan fi tunawa da shi, wanda kuma zan yi koyi da su shi ne kula da ibada, domin ba za a taba zuwa masallaci ka gan shi a sahu na biyu ba, koda-yaushe a sahun farko za ka gan shi. In dai ibada ce, a gaba za ka gan shi; an shaide shi da haka”, in ji shi.
“Ina godiya ga yan Kannywood da sauran al’ummar da suka halarci jana’iza, wallahi har kwalla na yi saboda irin dandazon jama’a da na gani, Allah ya saka wa kowa da alhairi, sannan kuma ya ba mu hakurin rashin wannan mahaifi namu, muna fatan yadda ya samu kyakkyawar shaida a wajen mutane, ya sa ya samu wannan a can”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp