Sabon rantsatstsen ministan babban birnin tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike, ya shiga ofis domin kama aiki a ranar Litinin, inda ya yi gargadin cewa zai tsaya tsayin daka kan kafafunsa wajen gudanar da aikinsa domin kwato da dawo da asalin tsarin taswirar birnin tarayya Abuja.
A cewar Wike, dukkanin wani ko wasu da suka yi gini a muhallin da bai dace su yi gini ba, tun da wuri su kwan da sanin cewa za a fa a rashe wannan ginin babu makawa.
Ya ce, baya ga kokarin dawo da asalin zubin tsarin birnin tarayya da zai maida hankali a kai, zan yi aikin hadin guiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro mai inganci a cikin birnin tarayya.
Ya tabbatar wa mazauna FCT cewa zai yi duk mai yiyu wajen magance matsalolin tsaro da kuma tabbatar da doka da oda a tsarin bunkasa filaye da gine-gine.
“A shirye muke mu samar da kayan aiki ga dukkanin hukumomin tsaro domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
“Idan na samar da dukkanin abubuwan bukata ga hukumomin tsaro, ba zan amshi wani uzuri ba.
“Meye muke so, kawai sakamako, kuma dole hakan ya faru. Idan ba mu kare nan wajen ba, to muna cikin matsala kuwa.
“Ka ga mutane su saci wannan abun su saci wancan. Wake da alhaki? Ina jami’an tsaro suke? Dole a yi wani abu domin dakile hakan.
“Batun tsaro manufarmu ne baki daya. Shugaban kasa ya fada min, ko ma yaya ne dai, dole ne mu tabbatar da samar da tsaro ga Abuja, dole ne mu tabbatar ta samu kwanciyar hankali.
“Ba za mu lamunci dabi’ar ganin ko’ina ya zama kasuwanni ba. A’a, ba za mu amince da hakan ba. Eh, na sani abubuwan ba za su zo da sauki ba, amma ba shi ne ke nuni da cewa sai ka haifar da rikici ga wasu mutane ba,” Wike ya shaida.
A wani mataki na gargadi, ministan ya gargadi dukkanin masu mamayar filaye ta hanyoyin da basu da cewa da cewa, “Idan kun san kun shimfida gini a inda bai kamata ku shinfida ba, ka sani gidanka fa dole ya sha kasa.”
Kazalika, ya gargadi masu bada gidajen haya ba bisa ka’ida ba, da su shiga taitayinsu. Kana ya nemi mutane da su ke mallakar shaidar mallaka (CofOs) na filayensu.
“Zan tsaya a kan yatsuna, na babban ma kuwa, kuma zan take naku kafafu da yatsun idan kuna yin ba daidai ba,” Wike ya tabbatar.