Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa wadanda ke daga tutar Rasha sun aikata laifin cin amanar kasa.
Janar Musa na magana ne jim kadan da kammala wata ganawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi da manyan jami’an tsaro a fadar Aso Rock a daidai lokacin da dimbin matasa ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna bacin rai kan tsadar rayuwa.
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Kasuwar Dodoru A Jihar Kebbi, Rumfuna Da Yawa Sun Lalace
- Yaduwar Fasahar Juncao Ta Nuna Sahihancin Sin
A cewar babban hafsan tsaron, doka za ta yi aiki a kan duk wanda aka samu da aikata wannan laifin na daga tutar Rasha a yayin gudanar da zanga-zangar.
Kazalika, Janar Musa ya gargadi waranda ke kiraye-kiyaren juyin mulki a kasar, yana mai cewa, rundunar soji ta amince da tsarin dimokuradiyya, don haka babu yadda za a yi sake a samu sauyin gwamnati.
Ita ma gwamnatin Rasha ta nesanta kanta daga wannan mataki na daga tutarta a yayin zanga-zangar.
Ta jaddada cewa, ko kadan ba ta da hannu a cikin abin da ke wakana a fadin Nijeriya.