Junaidu Abdullahi, wanda aka fi sani da Abusalma a TikTok, an kama shi kuma an miƙa shi gidan yari saboda kiran zanga-zanga kan matsalar tattalin arziki a Nijeriya.
Kama Abusalma ya biyo bayan wani bidiyo da ya yaɗu inda ya yi kira ga mutane su gudanar da zanga-zanga kan ƙarin farashin kayayyaki da kuma zagin shugabannin addini da suka yi adawa da zanga-zangar.
- Gwamnan Kano Ya Kwace Filayen Makarantun Da Ganduje Ya Cefarnar
- Rikicin Masarautar Kano: Sarki Bayero Ya Fara Bayyana A Bainar Jama’a A Kano
Jami’an tsaron sun fara tsare shi ne a ranar Jumma’a daga nan aka kai shi a gidan yari na Kurmawa a Jihar Kano.
A cewar wani ɗan uwansa mai suna Mustapha Hamza, Abusalma ya ɓace bayan samun wani kiran wayar gaggawa amma daga bisani an gano shi a hannun hukuma.
An ɗage shari’ar sa zuwa makonni uku, amma har yanzu dai ‘yan sanda ba su bayar da wani jawabi ba kan lamarin.
Ƙungiyar Amnesty International ta yi tir da kama shi, kuma ta nemi a saki Abusalma nan take haka kuma tana zargin gwamnatin Nijeriya da hukunta shi saboda amfani da haƙƙinsa na yin zanga-zanga.
Amnesty International ta zargi kama Abusalma da yin kama da hanyar da ake amfani da ita wajen kawar da masu adawa a cikin halin talauci da yunwa mai tsanani.