Wata gagarumar zanga-zanga ta barke a Jos, babban birnin jihar Filato, biyo bayan nasarar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dr Nentawe Yilwatda Goshwe ya samu a kan gwamnan jam’iyyar PDP, Caleb Mutfwang a hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Kotun daukaka kara ta yanke hukuncin soke zaben Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang kan rashin tsari da kuma rashin bin umarnin Kotu.
- Hadaddiyar Tawagar Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Za Ta Ziyarci Kasar Sin
- Dalilan Da Suka Sa Turawa Samun Nasarar Mulkin Mallaka A Arewa
Kafin yanke hukuncin a ranar Lahadi, an tsaurara matakan tsaro a dukkan muhimman wurare a babban birnin jihar domin dakile duk wata barazanar tsaro.
Amma duk da haka, bayan samun labarin hukuncin kotun, cece-ku-ce ta mamaye jihar yayin da aka ga jama’a tawaga-tawaga suna tattaunawa kan hukuncin.
A karamar hukumar Jos ta Kudu, matasan da ke goyon bayan PDP sun yi dafifi a zagayen Gyel da dama domin nuna rashin jin dadinsu kan hukuncin.
An kuma yi irin wannan zanga-zangar a mahadar Angwan Rukubu da ke Jos ta Arewa da karamar hukumar Riyom ta babban birnin jihar.