Fadar shugaban kasa a yammacin ranar Talata, ta bayyana cewa, shugaba Bola Tinubu ya damu matuka da tashin farashin kayayyakin abinci a kasar nan, ya kuma umurci kwamitin shugaban kasa kan bada agajin gaggawa da ya dauki matakin gaggawa domin lalubo mafita.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Malam Mohammed Idris ne ya bayyana hakan bayan taron kwamitin a ranar Talata a Abuja.
- Tsadar Rayuwa: Majalisar Wakilai Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Lalubo Mafita
- Mutane Sama Da Miliyan 43 Sun Kalli Bidiyon Dandanon Shirin Talibijin Na Murnar Bikin Bazara Na CMG Ta Kafar CNN
An gudanar da taron ne biyo bayan zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan kan hauhawar farashin kayan abinci a jihohin Neja da Kano.
Wasu masu zanga-zangar sun rufe wata babbar hanya a jihar Neja a ranar Litinin din da ta gabata domin nuna adawa da hauhawar farashin kayan abinci da ke ci gaba da hawa.
Haka kuma, wasu mata a Kano a makon da ya gabata sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin fulawa a jihar Kano.
Bayan ganawa da ‘yan kasuwar Kano a ranar Litinin, Gwamna Kabir Yusuf ya yi alkawarin sanar da shugaban kasar cewa ‘yan Nijeriya na cikin hali mawuyaci.
Idris ya shaidawa manema labarai a yammacin ranar Talata cewa, shugaba Tinubu ya damu matuka da yadda farashin kayayyaki ke hauhawa a fadin kasar nan.