A halin yanzu babban abin da ke ci wa mahukunta tuwo a kwarya shi ne yunkurin da wasu gamayyar kungiyoyin matasa suke yi na gangamin gudanar da zanga zanga na kwanaki goma a kasar nan a kan tsadar rayuwar da ake fama da ita.
Matasan, sun shirya fara zanga-zangar ne daga ranar 30 ga watan Yuli zuwa ranar 10 ga watan Agusta 2024. Babban dalilinsu na shirya zanga-zangar shi ne halin kunci da tsadar rayuwa da al’ummar kasar nan ke fuskanta, bisa yadda a kullum lamarin sai kara ta’azzara yake yi tun daga lokacin da Shugaba Tinubu ya janye tallafin man fetur a ranar da aka rantsar da shi, 29 ga watan Mayu, 2023.
Duk da cewa, babu wasu da suka fito karara suka nuna su ne masu daukar nauyin gudanar da, ana ganin yadda lamarin ya samu karbuwa musamman a kafafen sadarwa na zamani, ya sa gwamnati ta fara kiraye-kirayen lallai a dakatar da zanga-zangar, tare da bayar da hujjar cewa, bata gari da ’yan siyasa da ba sa yi wa kasa fatan alhairi na iya fakewa da zanga-zangar su aika laifuka tare da barnata kaddarorin gwamnati da na al’umma.
- Sheikh Daurawa Ya Yi Kira Ga Musulmi Da Su Nisanci Zanga-zanga Kan Adawa Da Tsadar Rayuwa
- Ba Za Mu Shiga Zanga-zangar Da Za A Yi Wa Tinubu Ba – Daliban Arewa
Ministan Yada Labarai, Alhaji Idris Mohammed Malagi, ya ce, babu wani dalilin shiga wata zanga-zanga domin gwamnati na sane da halin da al’umma ke ciki suna kuma daukar matakin dakile tsadar rayuwa da al’umma ke fuskanta.
Ya yi wannan bayanin ne a tattaunawarsa da manema labarai a fadar shugaban kasa ranar Litinin, inda ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya ta bayar da umarni na a fitar da tirela 1,740 na shinkafa domin raba wa jihohin kasar nan har da Abuja, tirela 20 kowannesu don rarraba wa al’umma mabukata.
ya ce , wannan na daga cikin matakan farko da aka shirya dauka, ana sa ran nan gaba kadan za a sake fito da kayan abinci domin a raba wa al’umma. Haka nan ya kara da cewa, sun kuma dauki matakan samar da cikakken tsaro ga manoma domin su samu damar ci gaba da noma ba tare da tsoron ayyukan ‘yan ta’adda ba.
Minista Idris Malagi ya karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa, wai gwamnati ta raba wa Malamai miliyan 16 domin su yi kokarin shawo kan matasa masu shirya zanga-zanga, yana mai bayyana cewa, wannan maganar karya ce tsagwaronta.
“A kullum gwamnati na tattaunawa da Malamai a kan yadda za a ciyar da kasa gaba, kuma har yanzu a kan haka muke” in ji shi.
A wani bangare kuma, jami’an tsaro sun gargadi masu shirin zanga-zangar da su gaggauta janye aniyarsu. Rundunar ‘yansanda na Jihar Kaduna ta fitar da takardar sanarwar jaddada dokar haramta zanga-zanga a fadin jihar. Sanarwa ta ce, doka za ta yi aikin ta a kan duk wanda ya karya dokar hana zanga-zanga, ta kuma umarci al’ummar jihar su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da fargaba ba.
Duk da wasu malaman addinin musulunci suna kira da a kauce wa shiga zanga-zangar, Shehin malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Kaduna, Sheikh Dakta Mahmud Abubakar Gumi ya ce, ‘yan siyasa da mahukunta ba sa jin wa’azi da jawo hankalin da malamai suke yi musu, saboda haka abin nan da matasa ke shirin yi na zanga-zanga shi ne suka fi jin tsoro, saboda haka ya kamata a goya musu baya, a kan haka bai kamata a rika bayar da tsoro da abin da ke faruwa a kasashe irin su Sudan, Labanon Libiya da sauransu ba, “Su can kabila daya kadai ne suke da shi, ba kamar Nijeriya ba da ake da banbanci kalakala.”
Ya kumu nemi matasan su tsara abin da suke bukata gwamnati ta yi domin saukaka radadin da ake fuskanta, ka da su nemi abin da ba zai yiwu ba, “Ku yi a cikin tsari ba tare da cutar da wani ba, ka da kuma ka kai kanka ga wata cuta, muna goyon bayan zanga-zangar ne saboda yaren da gwamnatin ta fi fahimta ke nan” in ji.
A tattaunawar da wakilimu ya yi da daya daga cikin masu shirya zanga-zangar, Kwamrade Yahaya M. Abudllahi na Kungiyar ‘Arewa Youth Ambassadors’ ya bayyana cewa, suna nan a kan bakansu, babu gudu babu ja da baya, “Shirin zanga-zangar ya samu karbuwa, al’umma za su fito a jihohin Kaduna, Bauchi Kano, Ribas, Imo Legas da wasu sassan Nijeriya, mun gaji da wannan tsadar rayuwar da muke ciki, dole gwamnati ta dauki matakan saukaka wa al’umma” in ji shi.
Ya kara da cewa, wasu kungiyoyin matasa sun nuna aniyarsa ta shiga zanga-zangar. A kan batun neman izinin jami’an tsaro, ya ce, “Babu inda aka rubuta a cikin kundin dokokin kasar nan cewa, sai al’umma sun nemi izini kafin su yi zanga-zangar lumana, za mu fito mu bayyana bacin ranmu cikin natsuwa ba tare da barnata duniyar kowa ba, in har kun ga wani yana barna to an turo shi ne, ba a cikin mu yake ba”
“Wannan matsin rayuwar ya shafi kowa ba tare da banbancin kabila, addini, ko siyasa ba, saboda haka duk wanda ya ji lamarin ya dame shi to mu hadu a titi”, in ji shi.
Jihar Kano na cikin jihohin da ake jin tsoron wannan zanga-zanga, musamman saboda wasu abubuwa da ake ganin na iya zama wani dandamalin huce haushin masu fushi da fushin wasu. Musamman idan aka yi la’akari da yawan al’ummar Kano sannan kuma akwai bakin- haure daga wasu kasashe da kuma wasu jihohi da suke neman halaiyarsu wadanda ba dole su yi wa lamarin zanga-zangar kyakkyawar fahimta ba.
Wadanda suka fi mararin gudanar da zanga-zangar a Jihar Kano ba su wuce matasa ‘yan bana bakwai ba, sai ‘yan ta fashe kowa ya samu da kuma kalilan wadanda abubuwan da kasa ciki ke matukar ci masu tuwo a kwarya. Hakan ta sa ake tsoron tsunduma cikin wannan zanga-zangar domin ba dole ta iya haifar da da mai ido ba.
Ana ganin cewa batun siyasa a Jihar Kano zai taka gagarumar rawa a lokacin zanga-zangar idan ta yiwu, musamman ganin yadda ake fama da kika-kaka a kan rikicin masarauta tsakanin Kwankwasawa da Gandujiyawa.
Haka kuma sarkakiyar da ta dabaibaye rikicin na masarautun Kano, da a halin yanzu ana shafe kusan watanni biyu kenan sarakuna biyu kowa na jan zarensa da sunan shi ne halattaccen sarkin Kano, duk da irin hukunce-hukuncen da kotuna daban-dabban suka zartar kan matsalar. Amma har yanzu ba a rabu da bukar ba.
Wadannan dama wasu batutuwa na cikin abubuwan da ake ganin na iya ruruta wutar zanga-zangar domin huce haushi ko kuma kokarin amfani da zanga-zangar wajen sace-sacen kayan jama’a da sunan “ganima”, musamman yadda ta faru a lokacin da gwamnati mai ci ta ba da umarnin rushe wasu kantuna a filin Idin Kano da ke kofar Mata.
Bugu da kari, an ga yadda wasu matasa suka yi amfani da irin wannan murna wajen afka wa kadarorin wadanda ba su ji ba kuma ba su gani ba.
Tsananin talauci da tsadar rayuwa na cikin abubuwan da ka iya bata kyakkyawar niyyar da aka shirya zanga-zangar domin ta, musamman a halin yanzu da cin abinci sau biyu ya gagari wasu rukunonin al’umma a jihar da ke da yawan al’ummar da suka tasamma Miliyan 20. Haka nan, irin hasadar da wasu mara shi ke yi ga masu shi, ita ma babbar barazana ce ga batun batun zanga-zangar da ake shirin gudanarwa.
Ana gudun da zarar an tsunduma cikin zanga-zangar wasu na iya fakewa da ita su ci karensu babu babbaka. Fargabar wannan ta sa wasu malamai ke ganin kamata ya yi a samu wata dabarar fadakar da gwamnati halin da ake ciki amma ba zanga-zanga ba.
Daya daga cikinsu, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Fanisau kuma sakataren Majalisar Mahaddata Alkur’ani a Jihar Jigawa, Sheikh Nasiru Haruna ya bayyana yadda yake kallon wannan yunkuri da ake na gudanar da zanga-zangar a fadin kasa.
Ya ce, “lallai akwai fargabar yin abin da bai dace ba a lokacin zanga-zangar, amma kuma ko shakka babu akwai bukatar a tunatar da gwamnatin halin da al’ummar kasa ke ciki, musamman batun tsadar rayuwa, rashin tsaro da sauran al’amuran yau da kullum.”
A nata bangaren, Kungiyar Fityanul Islam ta nesanta kanta game da shirin zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, ustaz Sani ibn Salihu ya fitar wacce shugabanta Sheikh Dakta Muhammad Arabi AbulFathi ya sanya wa hannu a ranar 15 ga watan Yuli, 2024.
Kungiyar ta yi nuni da cewa, irin wannan gagarumin mataki da ake shirin dauka bai cika haifar wa al’umma alheri ba.
“Kungiyar Fityanul Islam ta Nijeriya ta nesanta kanta da irin wannan mataki na zanga-zanga domin za a iya samun marasa kishin kasa su tayar da tarzoma da ka iya haifar da rugujewar bin doka da oda.
“Don haka, Fityanul Islam ta Nijeria tana kira ga daukacin al’ummar musulmin kasar da su gujewa irin wannan zanga-zangar, maimakon haka, musulmi su yi azumi da addu’o’in neman taimakon Allah a dukkan masallatanmu. Mu yi saukar Al-Kur’ani mai girma sau miliyan cikin kwanaki goma da kuma tsunduma cikin Istighfar marasa adadi (Neman Gafarar Allah) don magance kalubalenmu.” In ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta sake bitar duk wasu tsare-tsare, musamman wadanda suka jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyaciyar rayuwa.
“Muna Addu’ar Allah ya kawo wa kasar mu mafita ya kawar da kalubalan da suka dabaibaye ta”, in ji sanarwar.
Hakazalika, Shugaban Hukumar Hisba ta Kano, Sheikh Aminu Daurawa shi ma ya nuni da rashin dacewar zanga-zangar, yana mai bayyana cewa, a bi komai cikin lalama ya fi a fito a yi abin da ba zai haifar da da mai ido ba.
Ita ma bangaren Kungiyar Izala bisa jagorancin Sheikh Bala Balau, ta nuna muhimmancin zaman lafiya tare da bin komai cikin kwanciyar hankali.