Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An Zargi Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da dibar wasu makudan kudade a wani banki ba bisa ka’ida ba. Tsohon Kwamishina na musamman a gwamnatin Dokta Rabiu Musa Kwankwaso,.Janar mai ritaya, Idris Bello Danbazau ne ya yi wannan zagin a yayin da yake gabatar da wata kididdiga da ya yi kan yadda aka debi kudin al’uma don amfanin kai.
Idris Bello Danbazau ya ce, akwai wasu makudan kudaee da gwamnatin Ganduje ta dauka daga asusun ajiya na Bankin Fidelity,ta wata boca mai lamba 0233, wanda aka yi amfani da ceki mai lamba 13757005 aka dauki zunzurutun kudi N150,000,000. a asusun bakin Fidelity mai lamba 5030025714.
Ya kara kafa hujja da cewa, akwai boca mai lamba 0373 aka dauki N100,000,000 ta amfani da ceki mai lamba 17599268 a asusun ajiyar Fidelity mai lamba 5030025714. Haka kuma akwai wata boca mai dauke da lamba 0351 da aka yi amfani da caki mai lamba 13757050 aka wawashi N200,000,000. An kuma debi N120,000,000 ta amfani da boca lamba 0372 da ceki mai lamba 17599068.
Duk kokarin da muka yi don jin ta bakin Kakakin Gwamnatin Kano ko Kwamishinan yada labarai, amma abin ya ci tura, domin ba su dauki waya ba.