Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce, zuwa yanzu ta kwato sama da naira biliyan talatinĀ daga hannun dakataccen Akanta-Janaral na kasa, Ahmed Idris.
Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa, shi ne ya shaida hakan a ganawarsa da ‘yan jarida a Abuja a ranar Alhamis, yayin da ke bayani filla-dilla kan irin nasarorin da hukumar ta cimma a shekarar 2022.
Daga cikin nasarorin da hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta samu daga watan Janairun 2022 zuwa Disamban 2022 har da farauto sama da naira N134,33,759,574.25, dalar Amurka 121,769,076.30, Fam 21,020.00, Yero 156,925.00, Kudaden kasar Sin 21,350.00, CEFA 300,000.00, hadi da wasu tulin kudaden da suka kwato.
Ya kuma ce, mutane sama da 3,615 ne suka shiga jerin binciken hukumar a wannan adadin lokacin bisa zargin tafka rashawa daban-daban, ya nanata cewa gwamnati mai ci ta maida hankali sosai wajen yaki da cin hanci da rashawa don haka ne aka samu nasarori sosai.
Bawa ya sanar da cewa a dukkanin fadin kasa za su yi gwanjon motocin da suka kwato da gidaje sama da 150 ga masu bukatar saya.
Bawa ya yi albashir da cewa daga lokacin da sashin musamman na yaki da satar kudi ta (SCMUL) ya fara aiki sosai, zai zama da wuya a samu kafar satar kudade a kasar nan.
Idan za a tuna dai hukumar EFCC na cigaba da zargin dakataccen Akanta-Janaral Ahmed Idris da yin sama da fadi da naira biliyan 109.