Alkalin kotun Tarayya da ke Abuja, Mai Shari’a, Halilu Yusuf, ya wanke tsohon muakadashin hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Ibrahim Magu da Fasto Emmanuel Omale mai kula da Cocin Divine akan zargin yin safafar naira miliyan 573.
Kutun ta yanke hukuncin ne a kan kara mai lamba FCT/HC/CV2541/2020 wacce Omale, matarsa da kuma Cocin suka shigar.
A lokacin binciken da kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa wanda Mai Shari’a Isa Salami ke jagoranta, ya yi Ikirarin cewa, binciken da sashen kwararru dake binciken kudi, NFIU ya gudanar, ya gano cewa, Magu ya tura naira miliyan 573 a cikin asusun banki na ajiyar kudaden Cocin Omale, inda aka yi amfani da kudaden don sayen wata kadara a kasar Dubai.
Amma a hukuncin da Halilu ya ce, shedar da aka gabatar a gaban kotun ta nuna cewa, rahoton da aka turawa NFIU a kan Asusun ajiyar banki na Omale, babu gaskiya aciki, kuskure ne.
Alkalin ya ce, kuskuren ya janyo bata wa Fasto Omale da kuma matarsa suna, har da ma rassan Cocin dake fadin duniya.
Alkalin ya kuma bayar da umarni da a biya naira miliyan 540 ga Cocin a matsayin diyyar bata suna.