Wata Kotun tarayya da ke Lagos ta bayar da umarnin kama Emmanuel Oku, wani ma’aikacin rukunin kamfanonin Dangote, bisa zargin damfarar kamfanin N735.248 miliyan.
Mai shari’a Deinde Dipeolu ya bayar da wannan umarni ne bayan buƙatar da jami’in shigar da kara, Mohammed Bello, ya gabatar, inda ya bayyana cewa Oku ya gaza halartar shari’ar bayan samun beli.
- Matatar Dangote Ta Rage Shigo Da Man Fetur Zuwa Najeriya, Ta Jefa Turai Cikin Rashin Tabbas – OPEC
- Dangote Ya Yabi Tinubu Kan Tasirin Yarjejeniyar Musanyar Fetur da Naira
Sashin yaƙi da Zamba na Rundunar ƴansanda (PSFU) da ke Ikoyi, Lagos, ya gurfanar da Oku tare da wasu mutane tara bisa zargin cinikayya ta hanyar damfara daga masu jigilar man fetur na Dangote zuwa matatun Ibese da Obajana. Masu laifin sun haɗa da Ikechukwu Kingsley Obi, Chigozie Chrisogonus Osukwu, da wasu karin mutum bakwai.
An ce waɗanda ake zargin sun damfari Dangote kimanin Naira biliyan 19 tsakanin Janairu 2022 da Yuni 2023. Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 25 da 27 ga Fabrairu don ci gaba da shari’a, inda aka umarci a kama Oku don gurfanar da shi gaban kotu.