‘Yansanda sun kama wasu matasa biyu, a jihar Adamawa, wadanda ake zarginsu da laifin kashe wani tsoho mai shekara 85, bisa zargin da suke yi masa na maita.
Matasan da aka kama bisa wannan zargin su ne, Gayawan Danzaria, mai shekara 22 da Thank-God Obadia mai shekara 18, wadanda suke zaune a garin Shimba da ke karamar hukumar Song.
A farkon wannan makon ne dai matasan suka gutsire kan wannan tsohon suka kai wa wata mata, wadda ta sa su yin hakan. Bayan yin wannan mummunan aiki sai asirinsu ya tonu.
An kama wadannan matasa, yanzu haka dai matar da ta sa su wannan aikin ta ranta a na kare.
Iyalan tsohon da aka kashe, sun ce matar da ta tura a kashe tsohon ta bayar da kudin shigar ciniki naira 20,000, ta yi alkawarin za ta cika musu naira 30,000 bayan sun kashe tsohon.
Kamar yadda majiyarmu ta ce, bayan sun karbi wasu daga cikin kudin, sai Thank-God ya saba gatari, suka nufi gidan wannan tsoho da misalin karfe 10:00 na safe, tare da Gayawan Danzaria.
Thank-God ya tabbatar da cewa sun samu marigayin ne a gidansa yana kwance, suka kai masa hari suka kashe shi ta hanyar gutsire masa kai.
Da yake tabbatar da labarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje,ya ce, wannan lamarin ya faru, kuma yanzu haka suna ci gaba da binciken wadanda ake zargin.
“Da zarar mun gama bincikar wadanda ake zargin za mu gurfanar da su gaban alkali,” Kamar yadda Nguroje ya tabbatar.