Tun da jimawa, mun sha ji, da ganin rahotanni dake zargin cewa wai mahukunta a kasar Sin na rushe masallatai, ko mayar da su wuraren aikata wasu harkoki na daban. Irin wadannan rahotanni da wasu kafofin watsa labaran yammacin duniya ke yadawa na da matukar hadari, kasancewar suna kunshe da zarge-zarge marasa tushe, da karairayi marasa shaidu na zahiri.
A baya bayan nan, wata kafar watsa labarai ta yammacin duniya ta rawaito zargin da hukumar kare hakkin dan’adam ta “Human Right Watch” ko HRW ta yi, cewa wai ana samun karuwar ruguza tsarin addinai a shekarun baya-bayan nan a kasar Sin, kuma wai Sin na kara azamar neman karfin iko kan addinai.
- Gwamnan Bauchi Ya Gabatar Da Biliyan 300 A Matsayin Kasafin Kudin 2024
- Kwace Wa NNPP Zaben Kano Na Iya Haddasa Tashin Hankali A Afrika – NNPP
Cikin wannan zargi akwai abubuwan lura da yawa, amma kadan daga cikinsu akwai batun rashin shaidu na hakika, ko korafi daga musulmin kasar dake zaune a wuraren da aka yi zargin. Wato dai idan har HRW na da gaskiya kan zargin da ta yi, kamata ya yi ta bayyana shaidun gani da ido, ba wai cewa wai “An gano daga hotunan tauraron dan Adam” ba!
Kaza lika da yake rahoton na HRW ya ce mahukuntan Sin na kokarin samun karin iko kan addinai, ba wai addinin musulunci kadai ba, abun tambayar shi ne wane irin iko ne Sin za ta samu idan ta dakile addinai da mabiyansu?
Ga duk mai son sanin ainihin gaskiyar halin da musulmi, da mabiya sauran addinai suke ciki a kasar Sin, hanya daya mafi sauki ita ce ya bibiyi rahotanni daga mazauna kasar, ko dai Sinawa ’yan kasa, ko baki mazauna kasar dake neman ilimi, ko gudanar da harkokin kasuwanci da sauransu, wadanda za su fadi gaskiyar lamari bisa abubuwan da suka gani da idanun su, ba wai jita-jita daga kafofin dake adawa da ci gaban kasar Sin ba.
Ko shakka babu kasar Sin na da tsare-tsare daban daban na kare kima, da martabar addinai, da hakkokin mabiya addinai bisa doka. Alal misali, a ranar 3 ga watan Afirilun shekarar 2018, ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayanai mai taken Manufofi da ayyukan Sin na kare ’yancin bin addinai”, wadda a ciki aka zayyana matakan da kasar ke bi na tabbatar da kowa ya yi addinin da ya zaba bisa radin kansa, da tabbatar da zaman jituwa tsakanin mabiya addinai daban daban, da ma wadanda ba sa bin kowane addini.
Kaza lika, takardar ta yi bayani filla-filla, game da matakan da Sin ke bi na tabbatar da an martaba ikon mabiya addinai na yin ibada ba tare da tsangwama ba, da inganta wuraren ibada, ta yadda mabiya addinai da wadanda ba sa bin kowane addini za su rayu cikin jituwa.
A nan birnin Beijing ga misali, akwai gwamman masallatai dake sassan gundumomin birnin daban daban, wadanda musulmi ke amfani da su a ko da yaushe don gudanar da ibada, kuma tsawon sama da shekaru 10 da nake halartar masallatan dake cikin birnin, ban taba ji ko ganin an rushe wani masallaci ba! Hakan ya tabbatar min da cewa akwai wasu boyayyu, kuma munanan manufofi, a zukatan masu kitsawa, da yada jita-jitar rushe masallatai a Sin.
Daga karshe akwai bukatar mu rika taka-tsantan da kafofin dake yada labaran karya domin cimma burin siyasa. Domin ko ba komai, sauraro da aiki da irin wadannan labarai na bogi, na iya haifar da rashin jituwa, da tada hankulan al’umma, da haifar da tashe-tashen hankula, musamman a irin wannan lokaci da duniya ta fi bukatar hadin kai, da zaman lafiya sama da kowane lokaci a tarihi.