Dan takarar da ke neman wakilcin al’ummar mazabar Kumbotso a majalisar dokokin tarayya a zaben 2023, Khalid Shettima Khalid ya bai wa shugaban kasa, Muhammad Buhari wa’adin sa’o’i 24 da ya dauki mataki a kan zargin da Honorabul Gudaji Kazaure ya yi kan zargin karkatar da Naira tiriliyan 89.
Khalid Shettima Khalid, ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai.
- Duk Wanda Ya Yake Ni Zai Gane Kurensa – Kwankwaso Ga Ganduje
- A Karo Na Farko Kudin Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Zarce Yuan Tiriliyan 40
Khalid wanda ya tsaya takarar dan majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar PRP.
Ya ce zargin da Honorabul Gudaji Kazaure ya yi yana da girma kuma binciken da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi shi ne ya zama wajibi a yi la’akari da halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
Ya ce badakalar da Honorabul Gudaji Kazaure ya bankado a babban bankin Nijeriya bai kamata a kunnen uwar shegu da ita ba.
“Mene ne tsoron mai girma shugaban kasa a kan zargin satar dukiyar kasa, nan da awanni 24 daga wannan bayanin za mu dauki matakin shari’a a kan Gwamnatin Tarayya idan har ba a yi wani abu ba, ta yaya wasu ‘yan kalilan za su sanya tattalin arzikin Nijeriya a aljihunsu,” cewar Shettima.
“Na damu da yadda ‘yan Nijeriya ke mutuwa da matsanancin talauci, mafi yawansu ba za su iya siyan magungunan Naira 500 ba saboda halin kuncin da muke ciki.”
Ya ci gaba da cewa abin takaici ne matuka yadda aka bar Honorabul Kazaure ya yi tonon sililin kuma gwamnati ta yi bincike ta bankado wadanda ke da hannu a aikata wannan aika-aika kuma a hukunta su idan kuma Gudaji Kazaure ya yi karya a kan wadanda ake zargin sun saci wannan makudan kudi shi ma a hukunta shi.