An dawo da yara 59 zuwa Kano da ‘yansanda suka kama bisa zargin cewa safararsu aka yi.
An mika yaran wadanda dukkansu ‘yan karamar hukumar Sumaila ne ga hukumar harkokin mata, yara da nakasassu ta jihar Kano.
- Yadda Mai Haihuwar Fari Za Ta Kula Da Kanta (4)
- Zamfara Ta Shirya Wa Kiwo, In Ji Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi
Babban sakataren hukumar, Muttaka Iliyasu Yakasai ne ya tarbi yaran a madadin kwamishiniyar hukumar, Hajiya Amina Abdullahi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, a ranar 6 ga watan Janairu ne rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja ta kama yaran masu shekaru tsakanin hudu zuwa 12 a lokacin da suke tafiya a cikin motar bas mai daukar mutane 15 a kan hanyar Abuja zuwa Kano.
Da farko dai, rundunar ‘yansanda sun sanya karar a matsayin wadanda ake zargi da safarar yara saboda rashin cikakkun takardu da kuma amincewar iyayen yaran.
Da yake jawabi a wajen taron amsar yaran, shugaban karamar hukumar Sumaila, Faruk Sumaila ya tabbatar da cewa, an tura yaran Abuja ne domin Almajirci amma ya jaddada illar da ke tattare da wannan yunkuri.