Gwamna Malam Umar A. Namadi, ya dakatar da Alhaji Aminu Kanta a matsayin kwamishinan ma’aikatar kasuwanci da kuma matsayin mamba a majalisar zartarwa ta jiha har zuwa lokacin da aka kammala gudanar da bincike kan zargin badakalar zagon kasa kan shirin ciyar da abinci a watan Ramadan a karamar hukumar Babura.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim.
- Jihohin Nijeriya 10 Da Ke Kan Gaba A Yawan Bashi
- Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Kashe Fiye Da Naira Biliyan 2 Domin Ciyarwa A Watan Ramadan
Sanarwar ta ce, matakin wani bangare ne na kudirin gwamnati na tabbatar da bin diddigin kudi da kuma tafiyar da kudaden gwamnati cikin tsari kuma yadda ya dace.
A cewar sanarwar, “Gwamnan ya bayar da umarnin dakatar da kwamishinan ne a wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim ya sanya wa hannu.”
Ya ce, an dakatar da Kwamishinan ne bisa zarginsa da hannu wajen zagon kasa ga shirin ciyar da buda baki a karamar hukumar Babura.
Dakatarwar ta fara aiki ne nan take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp