Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta ce cutar zazzabin lassa ta halaka mutum 154 a cikin jihohin 26 tun farkon shekarar da muke ciki.
A cikin rahoton yanayin cutar da cibiyar ta fitar a ranar Litinin, NCDC ta ce a cikin watanni hudun farko na 2023, an samu masu dauke da cutar 897.
- Ina Da Yakinin Samun Nasara A Kotu -Dan Takarar Gwamnan APC A Bauchi
- Dan Majalisar Dokokin Zimbabwe: Ba Za A Amince Da Leken Asirin Da Amurka Ta Yi Wa Babban Sakataren MDD Ba
Cibiyar ta ce jihohin da aka samu cutar sun hadar da Ondo da Edo da Bauchi da Taraba da Benuwe da Filato da Ebonyi da Nasarawa da Kogi da Taraba da Gombe da Enugu da Kano da Jigawa da sauransu.
Rahoton ya ce, “Tun daga satin farko zuwa 16 a wannan shekarar an samu mutuwar mutum 154”.
NCDC ta ce an samu kashi 72 cikin 100 da cutar a jihohi uku da suka hadar da Ondo da Edo da kuma Bauchi, inda ka samu kashi 28 daga jihohi 23.
Rahoton ya ce adadin masu dauke da cutar ya karu idan aka kwatanta da daidai wannan lokaci a shekarar 2022.