• English
  • Business News
Saturday, August 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
19 hours ago
in Dausayin Musulunci
0
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ziyarar ƙabarin Manzon Allah (SAW) tana daga cikin ibadu mafi girma da samun kusanci zuwa ga Allah (SWT). Babu wata ibada da ta kai darajar Manzon Allah (SAW) a wurin Allah. Babu wani abu da Musulmi zai yi Allah ya ji daɗi (yadda ya dace da shi SWT) kamar girmama Masoyinsa Manzon Allah (SAW). Domin girmama Manzon Allah, girmama Allah ne da ya aiko shi. Kuma ziyararsa (SAW), tana daga cikin girmama shi.

An karɓo Hadisi daga Ummul-Mu’umina Aisha (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ni ne cikamakon Annabawa, Masallacina ne cikamakon Masallatan Annabawa, shi ne mafi cancantar Masallacin da za a ɗaura kaya musamman don ziyartarsa.”

A nan, ba ana nufin cewa a ziyarci Masallacin ne muradi ba kawai, domin ai Masallacin ya ɗaran ma sauran Masallatau ne saboda kasancewarsa na Manzon Allah (SAW).

  • Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12
  • Sadaukantaka, Kunya Da Kawar Da Kai Na Annabi Muhammadu (SAW)

Hatta mu kanmu wannan al’ummar, mun samu darajojin da muka samu ne saboda kasancewarmu al’ummar Annabi (SAW). Allah ya saka wa Shehu Ibrahim Inyass da alheri, wanda ya ce “girman bawa, daidai girman ubangidansa ne.

Dukkan darajoji da martabobin da Allah ya baiwa Annabawa, ya tara wa Annabi (SAW) kuma ya ƙara ma sa da wasu na daban.

Labarai Masu Nasaba

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (4)

Idan aka dubi wannan, bai kamata a riƙa ɓata karatu ana cewa Masallaci ne za a ziyarta amma ba Annabi (SAW) ba. Ya kamata a gyara karatu, a gyara wannan fahimtar. Saboda irin wannan fahimtar ce ta haifar da a zamanin nan an samu rashin girmama Manzon Allah (SAW) har aka dasa bom kusa da shi. Ko ɗaga murya Allah ya hana a yi a gaban Annabi (SAW), to ina ga tada bom?

A huɗubar sallar Idil Fiɗir da Limamin Makka ya yi a Harami, ya ce Yahudawa ne suka tada bom ɗin, amma sai ga shi da Saudiyya ta nuna wanda ya yi abin, da sunanshi da kamanninsa har da dogon gemu, ɗan ƙasar ne mai iƙirarin bin Salafiyya Sunnah. Duk ire-iren karatuttukan nan ne na rashin ganin girman Annabi (SAW) suke jawo waɗannan bala’o’in. Ya kamata a ji tsoron Allah a gyara.

Malamai Malikawa sun yi hukuncin cewa zuwa ziyara a Madina wajibi ne ga wanda yake da hali. Ma’ana idan mutum ya yi Aikin Hajji, wajibi ne ya ziyarci Manzon Allah (SAW) idan yana da halin zuwa.

Masu cewa idan mutum ya yi Hajji shikenan ba sai ya tafi ziyarar ba, suna nuna alama ce ta ƙin Manzon Allah (SAW).

Hadisai masu yawa sun yi bayani a kan falalar ziyarar Manzon Allah (SAW).

Yana daga ciki, Abdullahi bin Umar (RA) ya ruwaito cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya yi Hajji, sai ya ziyarci ƙabarina bayan mutuwata, ya zama kamar wanda ya ziyarce ni ne lokacin da nake da rai.” Ma’ana duk ɗaya suke.

Asƙalani, mai sharhin Bukhari ya ce zuwa Madina iri biyu ne, ana zuwa a lokacin da Manzon Allah (SAW) yake raye a kan ƙasa domin a karɓi shiriya, bayan wafatinsa kuma a je a ziyarci ƙabarinsa (SAW).

Dukkanin malamai na Allah Ahlus Sunnah tun daga kan Sahabbai a kan wannan fahimtar suke.

Haka nan, Hadisi ya tabbata daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ziyarci ƙabarina, cetona ya cancanta a gare shi”. Abu Haraira (RA) ya ruwaito Hadisi daga Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu wani mutum da zai yi sallama a gare ni, face Allah ya dawo mun da raina har na amsa sallamar.”

Idan mutum zai je ziyarar, walau Alhaji ko wanda ba Alhaji ba, zai yi niyyar cewa zai je ya ziyarci Manzon Allah (SAW), sannan ya yi sallah a Masallacinsa, ya ziyarci sauran Sahabbai da wuraren Musulunci. Amma dai Annabi (SAW) ne a kan gaba.

Ana so idan mai ziyara ya tasam ma Madinar Annabi (SAW), ya yawaita salati ga Manzon Allah (SAW) domin ya ƙara samun haske da soyayyarsa (SAW).

Haka nan, ana so mutum ya yi wanka, ya sa turare, ya sa tufafinsa mafi kyau, kuma ya jaddada tubansa, sannan ya halarto da girman Annabi (SAW) a cikin zuciyarsa, da girman Sahabbansa, da ganin girman garin baki ɗaya (a matsayin wurin da Annabi (SAW) da Iyalansa da Sahabbansa suka rayu, da faruwar abubuwan tarihi na Musulunci. Lallai idan mutum ya yi haka, zai ji wani ƙarin imani har ya sa shi kuka.

Idan mai ziyara ya zo shiga Masallacin Annabi (SAW), ana so ya shiga da ƙafar dama ya ce “A’uzubillahil azim wa bi wajhihil karim wa sulɗanihil ƙadim minas shaiɗanir rajim, bismillah, allahumma salli ala Muhammadin wa alihi wa sallim, allahummagfirli zunubi waftahali abwaba rahmatika.”

Idan da hali ya yi ƙoƙari ya shiga Raula (wurin da Annabi ya ce Dausayin Aljanna ne) ya yi sallah nafila raka’a biyu a matsayin gaisuwar Masallaci. Idan kuma Raula ta cika, sai a yi sallar a duk wurin da aka samu a Masallacin.

Daga nan, idan lokacin ya kasance lokacin sallar farilla ne sai ya tsaya a kammala sallar, idan kuma ba lokacinta ne ba, yana idar da nafilar sai ya nufi ziyarar Annabi (SAW).

Idan ya zo wurin ƙabarin mai girma, sai ya baiwa alƙibla baya; ya fuskanci bangon ƙabarin kusa da inda hukuma ta amince a tsaya. Ya halarto da girman Annabi (SAW) tare da tunanin cewa ga fuskar Annabi (SAW) tana kallonsa. Sai ya yi sallama cikin ladabi na sarari da ɓoye, sannan ya yi salati ga Manzon Allah (SAW). Ma’ana ya ce”Assalamu alaika ya Rasulullah, assalamu alaika ya Nabiyyallah, assalamu alaika ya Khaira khalƙillah, assallamu alaika ya Habiballah, assalamu alaika ya Sayyidal Murasalin, assalamu alaika ya rasula Rabbul alamin, assalamu alaika ya ƙa’ida gurril muhajjalin. Ash’hadu an la’ilaha illallah wa ash’hadu annaka abduhu wa rasuluhu wa aminuhu wa khiratuhu Wa ash’hadu annaka ƙad ballagtar risalata wa addaital amanata wa nasahtal ummata wa jahada fillahi haƙƙa jihadihi.”

Sai mutum ya karanta ayar nan ta neman gafarar Allah a wurinsa (SAW) ta cikin Suratun Nisa’i. Idan ya samu hali sai ya ɗan ja baya kaɗan ya yi salati guda 70 ga Annabi (SAW).

Daga nan ya matsa daidai kamu ɗaya a dama, ya yi sallama ga Sayyidina Abubakar (RA), kuma ya ƙara matsawa irin haka duk dai a dama, ya yi sallama ga Sayyidina Umar (RA). Daga nan sai ya fice ya kammala ziyara.

Dangane da juya wa aklbla baya a kalli fuskar Annabi (SAW) lokacin da mutum zai yi addu’a, an ruwaito cewa Abu Ja’afarul Mansur Al-Abbas (Sarkin Musulmi) ya tambayi Imam Malik (RA) da ya zo ziyara cewa, “Shin Annabi (SAW) zan fuskanta in yi addu’a ko alƙibla?” Sai ya amsa ma sa da cewa “Don me za ka kawar da fuskarka ga Manzon Allah (SAW) alhali shi ne tsaninka kuma tsanin Babanka Adamu (AS) zuwa ga Allah?”. Saboda haka mai ziyara ya fuskanci Annabi (SAW) ya yi addu’a.

Amma da yake hukumar can ta yanzu ba su yarda a kalli Annabi (SAW) a yi addu’a ba, to sai mutum ya kalli Alƙibla sai ya halarto da shi (SAW) a zuciya. Kuma koda ma alƙiblar aka kalla dole sai an bi ta wurin Annabi saboda mutum zai yi salatinsa (SAW) a cikin addu’ar.

Akwai wasu da suke nuna wa Alhazai cewa ba koyaushe ne suka shiga Masallaci sai sun ziyarci Annabi (SAW) ba, suna kafa hujja da Hadisin da Annabi (SAW) ya ce “… kar ku sanya ƙabarina ya zamo wurin idi…”. A tasu fahimtar yin ziyararsa (SAW) koyaushe ya zama kamar Idi. To ba haka malamai suka fassara wannan Hadisin ba.

Ma’anar Hadisin in ji Malamai ita ce “kar a sanya ziyarar ƙabarin ta zama Idi wadda ba za a riƙa yi ba sai shekara-shekara.” Saboda dama Idi ba kullum ake yi ba, don haka Hadisin yana nufin kar a ƙi yin ziyarar har ya zama daga shekara sai shekara. Duk lokacin da aka samu iko a yi kawai.

Haka Malaman da ke da soyayyar Manzon Allah (SAW) a zuciyarsu suka fahimci Hadisin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AllahAnnabiManzo
ShareTweetSendShare
Previous Post

Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu

Next Post

Yara Uku Sun Gamu Da Ajalinsu A Wani Tafki A Borno

Related

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa
Dausayin Musulunci

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa

1 week ago
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (4)

2 weeks ago
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (3)

3 weeks ago
Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)

4 weeks ago
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (3)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (3)

1 month ago
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

2 months ago
Next Post
Yara Uku Sun Gamu Da Ajalinsu A Wani Tafki A Borno

Yara Uku Sun Gamu Da Ajalinsu A Wani Tafki A Borno

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Zanta Da Putin Ta Wayar Tarho

Xi Jinping Ya Zanta Da Putin Ta Wayar Tarho

August 8, 2025
Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka Sun Haɗa Gwiwa Don Wayar Da Kan ‘Yan Nijeriya Kan Sababbin Ƙa’idojin Samun Biza

Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka Sun Haɗa Gwiwa Don Wayar Da Kan ‘Yan Nijeriya Kan Sababbin Ƙa’idojin Samun Biza

August 8, 2025
Shin Amurka Ta Manta Da Azabar “Babban Koma-Baya” Tare Da Haraji Mafi Yawa a Lokacin Na Tsawon Kusan Karni?

Shin Amurka Ta Manta Da Azabar “Babban Koma-Baya” Tare Da Haraji Mafi Yawa a Lokacin Na Tsawon Kusan Karni?

August 8, 2025
Nijeriya Ta Horar Da Likitoci 360 Don Magance Mutuwar Mata Masu Juna Biyu

Nijeriya Ta Horar Da Likitoci 360 Don Magance Mutuwar Mata Masu Juna Biyu

August 8, 2025
Sin Ta Mika Sabon Kason Tallafin Abinci Ga Zimbabwe

Sin Ta Mika Sabon Kason Tallafin Abinci Ga Zimbabwe

August 8, 2025
Bashir Ojulari: Me Ya Sa Ake Tsoron Gaskiya Ta Yi Aiki A NNPC? 

Bashir Ojulari: Me Ya Sa Ake Tsoron Gaskiya Ta Yi Aiki A NNPC? 

August 8, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Amince Da Hutun Wata 6 Ga Mata Masu Shayarwa

Gwamnatin Kaduna Ta Amince Da Hutun Wata 6 Ga Mata Masu Shayarwa

August 8, 2025
’Yansanda Sun Kama ’Yan Bindiga 17 Tare Da Kashe 3 A Abuja

An Hallaka Manomi, An Kashe Shanu Da Tumakai A Wani Sabon Rikici A Bogoro

August 8, 2025
An Bude Taron Mutum-Mutumin Inji Na Duniya Na 2025 A Yau Juma’a

An Bude Taron Mutum-Mutumin Inji Na Duniya Na 2025 A Yau Juma’a

August 8, 2025
Bango Ya Kashe Mutum 6, Ya Raunata Wasu A Katsina

Bango Ya Kashe Mutum 6, Ya Raunata Wasu A Katsina

August 8, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.