Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ba da umarnin haramta sayar da man fetur a dukkan gidajen mai na ƙaramar hukumar Bama da garin Banki nan take.
Umarnin ya zo ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro na jihar, inda aka bayyana cewa matakin na ɗaya daga cikin dabarun gwamnati na yaƙi da ‘yan ta’adda.
- Zulum Ya Taya MNJTF Da Gwamnatin Alihini Bayan Harin Boko Haram A Wulgo
- Zulum Ya Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira 6,000 Garuruwansu A Borno
“Na ba da umarnin haramta sayar da fetur a garin Bama, Banki da sauran sassan ƙaramar hukumar Bama nan take,”
in ji Gwamna Zulum a wata sanarwa ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Dauda Iliya.
Ya yi kakkausan gargaɗin cewa duk wanda aka samu ya saɓawa wannan umarni za a yi masa abin da ya dace: “Babu wanda zai tsira. An ba hukumomin tsaro umarnin rufe duk wani gidan mai ko kama duk wanda ya karya wannan dokar.”
Gwamnan ya kuma jaddada aniyarsa ta tabbatar da zaman lafiya a jihar, yana kira ga jama’a da su ba da haɗin kai wajen yaƙi da ta’addanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp