Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya jagoranci wata tawagar manyan jami’an Nijeriya domin fara mayar da ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya tilasta musu tserewa zuwa Baga Sola da Jamhuriyar Chadi.
A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, mutanen da suka rasa muhallansu – mafi yawansu ‘yan asalin Borno ne – sun shafe kusan shekaru 10 a gudun hijira sakamakon rikicin da ya shafi yankin tafkin Chadi.
- Kwanaki Bayan Kashe Masunta 20, Boko Haram Ta Kashe Sojoji 20 A Borno
- Gwamnonin Tafkin Chadi Sun Yi Taro Karo Na 5 Don Magance Matsalar Yankin
Tawagar ta haɗa da Ministan harkokin jin ƙai da rage talauci, Dr. Yusuf Sununu, da Shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira da ƴan ci rani ta ƙasa. An tarɓe su a Baga Sola a ranar Laraba daga Gwamnan Yankin Lac, Saleh Tidjani.
Sanarwar ta bayyana cewa a matakin farko na aikin dawo da su, za a mayar da iyalai 1,768 da suka ƙunshi mutum 7,790 zuwa Najeriya.
Haka kuma, kafin fara aikin, Gwamna Zulum ya halarci rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatocin Nijeriya da Chadi, da hukumar kula da ƴan gudun hijira ta najalisar ɗinkin duniya (UNHCR) a Baga Sola.