A kokarin gwamnatin sa wajen sake farfado da jihar Borno, biyo bayan kalubalen matsalar tsaro na dogon lokaci, Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da wasu sabbin kudurorin ci gaba na tsawon shekaru 25, wadanda ya bayyana cewa aiwatar da su zai taimaka wajen dawo da jihar bisa hayyacin ta.
A lokacin da yake kaddamar da manufofin a ranar Asabar a birnin Maiduguri, Zulum ya ce wadannan kudurorin sun hada da ingantattun matakai da tsare-tsaren shekaru 10 wadanda gwamnatin shi za ta bai wa muhimmanci na karamin zango, matsakaici da dogon zango, a turbar sake farfado da jihar.
“Wadannan manufofin da kudurori ya kunsa wadanda za su tabbatar shekaru 10 masu zuwa, nan da 2030, za mu yi kokarin gyara mummunar barnar da matsalar tsaro ta haifar da kimanin kaso 70 cikin dari na adadin gine-gine da abubuwan tattalin arziki da more rayuwar al’ummar wannan jihar.
“Bugu da kari kuma, nan da shekaru 25 (2045) masu zuwa, za mu yi kokarin ganin mun dawo da al’amurra bisa ingantaciyyar turbar da za ta kasance ja-gaba a sha’anin harkokin noma da kasuwanci wanda zai hada hancin harkokin yan kasuwar kasashen Afrika-Ta-Tsakiya zuwa Kudu, gabar Tabkin Nile ya hada da gabashi zuwa arewacin Afrika.
A hannu guda kuma, Gwamnan ya bayyana wasu muhimman gadarko guda buyar dangane da wadannan kudurorin wadanda suka kunshi, gina ci gaban tunanin jama’a, ingantaccen tsari a harkar noma, bunkasa kiwon lafiya, alkinta muhalli ta hanyar da ta dace tare da farfado da kananan masana’antu da kasuwanci a matakin yankin, wanda ta haka ne ayyukan yi zasu bunkasa.
A nata bangare, Ministar kudi a Tarayyar Nijeriya, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, ta yaba matuka da wadannan sabbin kudurori da manufofi na gwamnatin jihar Borno, wanda ta bayyana a matsayin wadanda suka yi kan-kan-kan da na gwamnatin tarayya, na matsakaicin zango.
Shamsuna Ahmed, wadda sakataren din-din-din a ma’aikatar kudi, Alhaji Aliyu Shinkafi, ya wakilta ya bayyana kudurorin a matsayin wadanda suka zo a lokacin da jihar ke bukace da su.
Har wala yau, shima minista a ma’aikatar sadarwa da hanyoyin ci gaban tattalin arziki ta Nijeriya, Malam Isa Pantami, ya bayyana cewa wannan abin a yaba ne kuma mataki mafi muhimmanci a daidai irin wannan lokaci a jihar tare da yin kira ga al’ummar jihar Borno su bayar da cikakken goyon baya.