Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya nemi yafiyar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, kan harin da ake zargin wasu ‘yan bangar siyasa da ba a san ko su waye ba suka kai wa ayarin tawagarsa a jihar.
Wannan na zuwa ne daidai da ya sha alawashin cewa, a karkashin mulkinsa, ba zai bari duk wata jam’iyyar adawa a jihar ta ci zabe koda na mazaba daya ba a zaben 2023.
- Matan Kiristocin Arewa Sun Yi Wa Atiku Alkawarin Ruwan Kuri’a
- Sirikin Buhari Ya Fice Daga Jam’iyyar APC A Kaduna
Zulum, ya sanar da hakan a yayin da yake yi wa magoya bayan APC da masu ruwa da tsaki jawabi lokacin kaddamar da shugabanni da sakatarorin da kuma ‘ya’yan cibiyar yakin neman zabe a gidan gwamnatin jihar da ke a Maiduguri.
Ya ce, abin dariya ne ‘yan jihar da ke zaune a wasu garuruwa sama da shekaru hudu, suka fara yin tururuwa zuwa jihar a karkashin jam’iyyun adawa daban-daban, musaman PDP suka kuma fara neman goyon ‘yan jihar don zaben 2023.
A cewarsa, “Ina son na sanar da cewa, APC a karkashin mulkina, za ta tabbatar cewa, babu wata jam’iyyar adawa a jihar da za ta ci zabe a 2023”.
Ya kara da cewa, “abin takaici ne ganin wasu masu neman madafun iko a cikin mataciyyar PDP a jihar a yanzu suna shigowa Maiduguri da Naira 500,000 zuwa Naira 600,000, inda suke raba wa mutane don yin kamfen din bataci ga APC, bayan sun manta da cewa, Borno gidan APC ne.
Ya ce, “APC ba ta jin tsoron duk wata jam’iyyar adawa, musamman ganin cewa, APC a karkashin mulkinna a shekaru uku da suka wuce, mun yi kokari wajen samar da tsaro, ayyukan yi, tallafawa matasa da mata gina wa da kuma mayar da miliyoyin ‘yan gudun hijira zuwa matsagunan su na ainahin.”