A wani bangare na ayyukan jin kai a ziyarar kwanaki biyu a karamar hukumar Ngala, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Lahadi ya raba Naira miliyan 255, da kayan abinci da turamen atamfa ga maras galihu kimanin mutum 70,000.
An gudanar da raba kayayyakin ne a wurare uku: garin Ngala, Gamboru da Wulgo, dukkansu a karamar hukumar Ngala, wanda ya hada maza da mata wadanda suka ci gajiyar tallafin.
Tun a ranar Jummu’a Gwamna Zulum ya isa Gamboru inda ya shafe dare biyu yana gudanar da ayyukan jinkai da sauran ayyukan ci gaban yankin.
Gwamna Zulum ya ce, “Yawancin al’ummar karamar hukumar Ngala sun fuskanci ibtila’in ambaliyar ruwa wanda ya lalata gidaje da gonaki. Wanda hakan ya tilasta dole gwamnati ta sa hannu don rage tasirin matsalolin da jama’a ke fuskanta, kuma zamu ci gaba da tallafa wa mutanenmu da ke cikin bukata har sai sun samu damar tsayawa da kafafunsu.” in shi.
Kafin raba kayan abinci, tsabar kudi tare da turamen atamfa, Gwamna Zulum a ranar Asabar ya sake bude Kasuwar Shanu ta kasa da kasa ta Gamboru wadda aka rufe kusan shekaru 7 saboda ayyukan Boko Haram.
Wanda nan take manyan motocin dakon kaya na tireloli suka fara dakom dabbobi, daga kasuwar Gamboru zuwa Maiduguri da sauran sassan Nijeriya.
Gwamna Zulum ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa gagarumin kokari tare da shugabanci nagari, wanda ya haifar da zaman lafiya a Borno da fadin kasar nan baki daya.
A hannu guda kuma, Gwamna Zulum ya yaba wa sojojin Nijeriya hadi da sauran jami’an tsaro bisa sadaukarwar da suka nuna wajen samar da yanayi mai kyau da ya ba da damar maido da harkokin tattalin arziki a fadin jihar Borno.