Gwaman Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara ga iyalan masunta sama da 30 da ‘yan Boko Haram suka kashe a kauyen Mukdolo.
A wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa Twitter, ya ce ya je garin Dikwa inda daga nan ne masuntan ke zuwa sana’ar tasu inda mayakan Boko Haram suka yi musu kwantan bauna, domin jajanta wa iyalan mamatan.
- Mutum 2 Sun Shiga Hannu Kan Yi Wa Mace Kurma Fyade A Jihar NasarawaÂ
- Mayakan Boko Haram 443 Sun Mika Wuya Yayin Da ISWAP Ta Kashe Musu Sama Da Mutum 300
Karamar hukumar Dikwa na daga cikin kananan hukumomin da Boko Haram ta mamaye a shekarar 2014 kafin sojoji su kore su tare da kwace garin.
Gwamnan ya gana da iyalan mamatan a fadar Shehun Dikwa Alhaji Ibrahim Ibn Ibrahim El-Kanemi.
Zulum ya kuma jajanta wa iyalan tare da yin addu’ar neman rahama ga mamatan.
“A madadin gwamnati da mutane, ina mika sakon ta’aziya ga iyalai da ‘yan uwan mamatan wadanda aka kashe a kokarinsu na neman na kansu domin ciyar da iyalansu”.
Sanarwar ta kara da cewa gwaman ya bayar da tallafi ga iyalan mamatan a lokacin ziyarar.