Zuwa Kasuwar Rimi Ya Fi Min Wahala Akan Zuwa Dubai – Rashida Mai Sa’a

Rashida Mai Sa’a

Daga Abdullahi Muhammad Sheka Kano

Tsohuwar fittacciyar jarumar fina-finan Hausa Rashida Abdullahi ta bayyana cewa zuwa kasuwar Rimi da ke birnin Kano ta fi ma ta wahala a kan zuwa kasar hadaddiyar Daular Larabawa wato Dubai.

Rashida Abdullahi Adamu  wadda aka fi sani da Rashida mai sa’a, ta bayyana hakan ne a cikin wata hira ta musamman da ta yi da sashen Hausa na BBC.

“Wasu suna zargin ina yi musu hassada a kan bidiyon da na ke a Dubai. Wallahi ni ba wanda ya isa na yi masa hassada, domin ni Dubai tun suna ‘yan yara wadanda su ka je a wannan lokacin, ba su ma yi wayo ba na ke zuwa Dubai”

“Dan ni kamar yadda na fada a wancan lokacin kamar kasuwar Rimi ma ta fi min Dubai wahalar zuwa, saboda kasuwar Rimi sai in dade ina son in je amma ban je ba. Amma Dubai ina kwance a kan gado na zan sayi ticket di na online a turamin da bizata na je nayi firintin na je na hau jirgi na yi tafiyata”

Haka kuma jarumar ta kara da cewa ta dauki zuwa kasar Dubai kamar inda ta ke zuwa ta kai dinki da sauran ‘yan saye–saye, ba wai kasar hutu ba kamar yadda wasu ke zuwa.

“Ni na dauki Dubai kamar inda na ke zuwa na kai dinki in dan siyo wasu ‘yan kayayyaki haka, ba wai in je in yi hoto ko in huta ba”

“Idan kana son ka huta tafi London ko Amurka ko Spain ko Germany ko Paris, shi ne na san wadannan wuraren hutu. Amma nima da in je Dubai in huta ai gwara in je Nijar dan zan ga rakuma”

Rashida Adamu Abdullahi tsohuwar mai baiwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shawara ce kan harkokin mata, tace Kasar Dubai dai na karbar bakuncin dubban ‘yan Nijeriya da kan je don yawon shakatawa ko harkokin kasuwanci wasu kuma suna zuwa ne domin duba lafiyarsu.

 

 

 

 

 

Za A Iya Yin Amfani Da  Fannin Wasanni Don Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya – Zailani

Daga Abubakar Abba, Kaduna

 

Shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna Yusuf Ibrahim Zailani ya bayyana cewa, yin amfani da fannin wasanni zai  taimaka wajen kawo karshen ta’addanci, sace mutane da sauran nau’ukan rashin tsaro a Nijeriya.

Zailani ya bayyana hakan ne a cikin sanasawr da hadimin yada labaransa Ibrahim Dahiru Danfulani ya fitar a Kaduna.

Shugaban ya bayyana hakan a jawabinsa a taron bita na kwana uku kan danarun bayar da horo kan wasanni da hadiminsa na matsa da wasni da al’adu Ekene Abubakar Adams ya shirya a filin wasa na Ahmadu Bello Stadium da ke  a jihar Kaduna.

Ya bayyana cewa, taron bitar wani Karin ci gaba ne ga gwamnatin Malam Nasir el-Rufai wajen kara samar da ayyukan yi a tsakanin matsa.

Shugaban majalisar ya yi nuni da cewa, akwai matukar bukatar a yi tunani sosai domin kawo karshen rashin tsaron day a addabi kasar nan.

A cewar Zailani ya kara da cewa, akwai bukatar a fito da hanyoyi, musaman ta hanyar yin amfani da tattalin arziki domin samarwar ciyar da rayuwar matsana da ke a kasar nan gaba da kuma samar wa da ‘yan Nijeriya abincin da za su ci suda iyalansu.

Shugaban ya kuma bayyana cewa, baya mahimmancin da wasanni suke das hi, suna kuma kara kiwon lafiyar ‘yan adam tare da kuma samar wa wadanda suka rungumi fannin da kudaden shiga.

Zailani ya bayyana cewa a lokacin da Ekene Abubakar Adams ya tuntube shi kan shirya bitra nan take ya amince da ita, musamman ganin alfanun da yin hakan yake das hi a tsakanin matsa da kuma kasa baki daya..

Shugaban majalisar  ya kuma yi kira ga mahalarta was an dasu yi amfani da darasin da suka koya domin ciyar da rayuwarsu gaba.

Zailani  ya ce, “Ina da yakinin cewa, wadanda za su gudanar da aikin da suka zo daga  Cibiyar wasanni ta kasa (NIS) hazikai ne kuma takardar shedar da mahalarta taron za su samu, za su iya amfani da ita a daukacin fadin duniya.”

 

Amina Mohammed Ta Sake Zama Mataimakiyar Babbar Sakataren MDD

Daga Khalid Idris Doya

A shekaran jiya ne Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya sake zabin Amina Mohammed a matsayin mataimakiyar babban sakatare na Majalisar, jim kadan bayan da majalisar ta sake zabin Guterres a karo na biyu.

Amina wacce tsohowar ministar muhalli ta Nijeriya ce kuma ‘yar asalin jihar Gombe ta samu goyon baya sosai daga al’umman Nijeriya kan wannan nadin.

Guterres da Amina za su fara sabon wa’adi a farkon watan Janairun 2022.

Antonio Guterres ya gaji Ban Ki-moon ne a watan Janairun 2017 kafin Donald Trump ya zama shugaban Amurka wanda ya sha caccakar Majalisar Dinkin Duniya.

Da ya ke ganawa da ‘yan jarida bayan shan rantsuwar kama aiki a karo na biyu, Guterres ya bayyana cewar ya zabi ci gaba da tafiya tare da Amina a karo na biyu bisa gamsuwa da salonta da kokarinta.

“Bayan zabi na, na sake amincewa mu cigaba da aiki tare da sakatare Janar ina fatan za ta amince da wannan damar da na bata,” inji shi.

Amina wacce take tsaye a gefen Guterres lokacin gaanwa da ‘yan jaridan, ta amince da wannan damar da ta samu hannu biyu-biyu.

Amina ‘yar asalin jihar Gombe ce amma haihaffiyar kasar London ce. Ta kasance jaruma a bangaren deflomasiyya kuma ‘yar siyasa mai nagarta, bisa haka muka dauko tarihinta domin ku kara saninta.

Tun daga 2002 har zuwa 2005 Amina ta yi Ko’odinetin shirin ilimin mata na Majalisar Dinkin Duniya na karni. Ta kasance mai taimaka wa Nijeriya ta fuskacin tsare-tsaren yadda za a fita daga kangin talauci da kyautata rayuwar jama’a, ta kuma zama mai nema wa mata ‘yanci da hakkinsu a kowani lokaci.

A 2012, Amina ta zama jigo wajen gudanar da jadawalin tsarin cigaba na Post-2015 D-Agenda, ta kuma kasance babban mai bada shawara wa sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon a kan aiwatar da tsarin cigaba na 2015. A wannan damar da ta samu, tauraronta ya cilla, ta yi aiki a matsayin jami’ar hada Sakatare Janar da fitattun mutane (HLP), da babban taron bude aiki (OWG) tare da masu ruwa da tsaki. A 2014, ta yi aiki a matsayin mai bada shawara wa kwamitin sakataren janar kan samar da sauye-sauye don daurewar cigaba.

A shekarar 2015 zuwa 2017 Amina Mohammed ta rike Ministan muhalli a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari daga watan Nuwamban 2015 zuwa Fabrairun 2017. A wancan lokacin ta wakilci Nijeriya tarayyar Afrika (AU) a kwamitin gyara wanda Paul Kagame ya jagoranta. Ta yi murabus a matsayin mambar majalisar zartaswar Nijeriya a ranar 24 ga watan Fabrairun 2017.

A watan Janairun 2017 Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteeres ya sanar da nadin Amina Muhammad a matsayin mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya gaba daya. Wanda kuma shekaran jiya ya sake zabinta a karo na biyu.

 

 

 

Exit mobile version