Tsohon Mai Baiwa Trump Shawara Ya Amsa Laifin Yin Karya

15

Daga Rabi’u Ali Indabawa

Tsohon mai bai wa shugaba Donald Trump shawara kan tsaro, Micheal Flynn, ya amsa laifi yau game da yin karya ga hukumar bincike dangane da alakarsa da Jakadan Rasha a Amurka.

Amsa laifin da ya yi ya nuna irin hadin kan da shi Flynn ke bayarwa a binciken katsalandan Rasha a zaben Amurka da mai shigar da kara na musamman Robert Mueller ke yi.

An tuhumi Flynn da yin karya kan wata boyayyar tattaunawa da yayi da jakadan Rasha na wancan lokacin a Amurka, Sergey Kislyak. A wata takarda da kotu ta fitar ranar jumma’a ya nuna yadda ya tattauna da jakadan kan takunkumin da Amurka ta dora kan Rasha karkashin Gwamnatin tsohon Shugaba Barack Obama.

Takardar ta nuna cewa a watan Janairu, “da gangan” Flynn ya furta bayanan karya da yaudara ga masu bincike dangane da tattaunawarsa da jakadan Rasha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here