Atiku Ya Yi Yekuwar Kwance Wa APC Zane A Kasuwa

748

Daga Muhammad Maitela, Abuja

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi kira ga magoya bayan sa tare takwarorin sa da suka bar jam’iyyar PDP a baya, da cewa su yi gaggawar yiwa jam’iyyar APC tawaye, tare da dawowa tsohuwar jam’iyyar su ta asali, ya ce hakan ne zai bayar da damar kwace mulkin Nijeriya daga hannun jam’iyya mai ci yanzu ta APC a zaben 2019.

Alhaji Atiku ya bayyana jam’iyyar PDP a matsayin jam’iyya kwaya daya wadda kowanne dan kasa ya shaidi yadda ta tabuka abin a zo a gani ta fannin kyakkyawan mulki da ciyar da kasar nan gaba, wanda wata gwamnati ta kasa samar da rabin sa.

Wazirin Adamawa, wanda ya caccaki jam’iyyar APC da gazawa, a lokacin da ya kai ziyarar sa ta farko a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Abuja, bayan shelanta dawowar sa cikin jam’iyyar. Ya ce, babu yadda za a yi a kwatanta mulkin APC da matsayi na rabin abinda PDP ta samar na kyakkawan shugbanci a lokacin zamanin da tayi mulkin Nijeriya.

Ya ce “bari in sake bayyana muku cewa, nasarorin da gwamnatin PDP wadda ta gabata ta samar a kasar nan su kadai ya isa in sake yin kira gareku kan cewa ya zama dole ku dawo gida, irin yadda na yi. Saboda wannan ita ce hanya kwaya daya da zata ba sauran abokanan tafiyar mu su dawo gida domin sake gina ta bayan mun dunkulewa wuri guda. Kuma sai an samu irin wannan yunkurin ne PDP zata sake karbar gwamnati, ta ci gaba wajen aikin ta na shayar da yan Nijeriya romon dimokuradiyya.

“zan sake jaddada muku cewa, bisa ga hakikanin gaskiya hobbasar da gwamnatin PDP ta yi, wajen samar da kyakkyawan shugabanci a kasar nan, har yanzu ba a yi wata gwamnati a kasar nan ba, wadda ta doshi rabin kokarin abinda PDP ba”.

Atiku ya kara bayyana cewa dawowar tsuffin yayan jam’iyyar PDP; wadanda suka bar ta a baya, shi ne babban yunkuri da alamar kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC a shekarar 2019. Saboda yadda ta gaza wajen cika alkawuran da ta dauka wa yan Nijeriya.

Da yake marhabin da zuwan Wazirin Adamawan a sakatariyar jam’iyyar; shugaban riko a PDP, Sanata Ahmed Makarfi ya bayyana canjin shekar tsohon mataimakin shugaban kasar a matsayin bude kofar ce dangane da tudadowar manyan yan siyasar Nijeriya zuwa PDP.

Ya ce wannan dawowa jam’iyyar da Atiku yayi wata babbar dama ce ga PDP kuma wadda zata dora jam’iyyar bisa kyakkyawar turba tare da dawo da martabar jam’iyyar wadda zata sahale mata dama wajen sake dare kujerar shugabacin kasar nan cikin sauki a babban zaben 2019. Duk da hakan, Makarfi ya musanta hannu-kasa tsakanin sa da dawowar Atikun.

“Ya Maigirma, ta dalilin ka kofofi da dama sun bude, PDP tana tsammanin dawowar manyan yayan ta da ta rasa da ma sabbin zuwa. Saboda haka, dole PDP ta kwana da wannan shirin kuma da shiri wajen ganin ta daidaita tsakanin yayan ta a cikin kowanne yanayi tare da kokarin yiwa kowa adalci a matakan taka muhimmiyar rawa dabandaban-daban. Wannan shi ne abinda ya kamata jam’iyyar PDP ta tsayu a kai, kuma shi ne ruhin da ya kamata ta rayu dashi”. Inji shi.

Makarfi ya bayyana wa Turakin Adamawa wasu daga cikin kalubalen da jam’iyyar PDP ta sha fama dasu, tare da kuma wasu daga cikin nasarorin da ta cimma a matakai daban-daban.

Bugu da kari kuma, a cikin tattaunawar da aka yi dashi ya bayyana cewa halin da ake ciki yanzu, shirye-shiryen babban taron PDP yana ci gaba da kankama.  Ya ce shugabanin jam’iyyar sun sha alwashin yiwa kowa adalci da kyakkyawan tsarin sakarwa kowanne dan takara mara.

Amma da aka bukaci Makarfi da ya fayyace zargin sasanta tsakanin yan takarar kujerar shugabacin jam’iyyar PDP na kasa, sai ya kada baki, ya ce shugabanin jam’iyyar basu da ta cewa dangane da wannan matsalar.

Amma dai ya ce “da farko yankin arewa sune suka fara bullo da zancen cewa a karkasa mukaman jam’iyyar zuwa shiyya-shiyya kuma an riga an cimma matsaya dangane da wannan. Jam’iyya ta amince da shi ba wai matsaya ce ta shugabanin rikon kwarya ba. Haka zalika kuma, yankin arewa sun zauna tare da ayyana wa kowacce jiha mukamin da ya kamata ta samu a siyasance.

“kuma wannan shi ne a siyasa ake kira cimma yarjejeniya a tsakani. Halin da kowanne bangaren yan siyasa suka amince zasu goyi bayan juna a lokacin zabe. Bugu da kari kuma, duk da akwai wadanda suka nuna turjiya dangane da wancan tsarin, kuma da yake siyasa ce ba a ce sun yi kuskure ba, dole a bar su dangal-gal kan ra’ayin su”. Ta bakin Makarfi.

A martanin shugaban jam’iyyar APC na kasa, dangane da wadannan kalaman, Cif John Odigie-Oyegun ya bayyana baran-baran din da Atiku yayi da jam’iyyar su ta APC bai kai wani batu na a tattauna a kan sa ba.

Oyegun ya furta martanin ne a lokacin da yake ganawa da wasu magoya bayan jam’iyyar APC a ofishin sa da ke Abuja, ya ce a iya sanin sa, a kasar nan babu wata jam’iyya mai tsari kamar APC. Ta bakin sa, ya ce” a kasar nan, duk mutumin da ya isa a kira shi cikakken mutum to zaka same shi a cikin jam’iyyar APC “.

Oyegun ya ce ficewar Atiku ba zai iya haifar tururuwar canja shekar yan jam’iyyar APC zuwa PDP ba, ballantana ya tayar da hankalin su.

“waye zai firgita da canja shekar tsohon mataimakin shugaban kasa, a matsayin wanda zai yi wani tasirin da har zai sa wasu yin gilgilwar bin zugar sa. An duk wanda ka ga ya canja sheka, to nauyin sa ya riga ya zagwanye tun ranar farkon, amma ba kamar wanda kowa ya ji shi ta hanyar shanun talla ba”.

“zai yi kyau idan mutum yana tafiya ya rinka kula da hagu da daman sa, wannan shi ne zai sa jama’a su rinka ganin ka da kima. Saboda haka babu wani jin abinda zai sa mu karaya kan cewa matakin zai jawo zurarewar jama’a daga barin mu, kuma bamu haufin wannan, to kai wa kake ganin zai yanki diron barin APC zuwa PDP ta dalilin Atiku? APC jam’iyya ce wadda a cikin kowacce rana sai habaka take yi”. Inji shi.

“APC jam’iyyar ce wadda ba ta da wata matsala a tsakanin yayan ta, amma ka kalli yadda PDP kullum a cikin hayaniya take. Jam’iyyar PDP da har yanzun nan ta kasa samun tsayayyen shugaba. Amma yau gashi nan ana kokarin sayen kujerar shugabacin ta da kudi. To yanzu da wannan ne kake tsammanin wani abu”.

“yanzu kana ganin hayaniya ce zata tsayarda PDP wuri guda, suna karaji ne da tunanin cewa har yanzu kan yan kasa bai waye ba; ina ai tuni kan mage ya waye. Al’amarin Nijeriya zai ci gaba da farfadowa kuma jam’iyyar ku ta APC zata ci gaba da bunkasa a kowacce safiya”. Ta bakin Odigie-Oyegun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here