Gyara A Kananan Hukumomin Jihar Kaduna: Cika Alkawari Ne Gwamna Ya Yi –Hon. Sa’idu Adamu

32

Daga Sulaiman Idris Bala

Babban mai ba Gwamnan jihar Kaduna Shahawara kan harkar yada labarai da dabaru, Hon. Sa’idu Adamu ya bayyana cewa gyaran da gwamnatin jihar ta ke yi a ’yan kwanakin nan, wanda wasu ke kallo kamar an kori ma’aikata ne ba bisa hakki ba, wannan wani alkawari ne da Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-rufai ya cika, wanda ya dauko tun lokacin da yake yakin neman zabe, na cewa in aka zabe shi zai kawo gyara a yadda Kananan Hukumomin ke tafiya.

Hon. Sa’adi Adamu ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa wakilan kafofin yada labarai da ke gidan gwamnatin karin bayani game da wannan mataki da ta dauka. Inda ya bayyana cewa ba an yi wannan abu ba ne don a ci mutuci ko a tozartar wani ba, illa iyaka an yi ne don a cika alkawarin da aka dauka, wanda ya ce kowa ya san yadda abubuwa suka lalace a Kananan Hukumomi, ta yadda komai bai tafiya yadda ya kamata.

Kakakin Gwamnan ya ci gaba da cewa Gwamna Nasiru El-rufai ya yi alkawarin cewa muddin aka zabe shi, to zai kawo kyakkyawan gyara a gurbataccen yanayin da Kananan Hukumomi ke ciki a jihar, ta yadda abin ya kai ma saboda lalacewa, hatta albashi Kananan Hukumomin ba sa iya biya har sai gwamnatin jihar ta tallafa masu, ballantana kuma su gudanar da wasu ayyukan ci gaban jama’a.

Ya ce, a wani bincke na musamaman da aka gudanar a wadannan Kananan Hukumomi, an gano cewa ma’aikatan bogi da wadanda ba sa aikin komai ne suka cika harkar albashinsu, ta yadda duk dan abin da Kananan Hukumomin ke samu suna tafiya ne wajen biyan albashin wadannan mutane, “to kuma ya kamata a sani cewa ba wai biyan albashi ne kadai aikin Kananan Hukumomi ba, akwai ayyukan ci gaban al’umma, wanda shi ma ya rataya ne a wiyarsu,” in ji Kakakin na Gwamna.

Alhaji Sa’idu Adamu ya ci gaba bayyana cewa a binciken da aka gudanar, akwai wasu Kananan Hukumomin da aka gano cewa sunayen ma’aikatan da ake biya albashi a duk wata, abin ya wuce hankali. Ya ce, “sai ka ga mutum yana karbar albashi a duk wata, amma ko ofis ba shi da shi, wasu ma a ma’aikatar ba su san shi ba, amma albashinsa da karin girma, ba wanmda ya tsaya. Sannan uwa-uba ga sunayen wadanda ma sam ba su a zahiri, wasu ne kawai ke kwashe albashin nasu.”

Don haka ya ce, irin wadannan abubuwa ne suka sa ya zama dole aka duba aka zabtare wadanda ake ganin ba a bukatarsu, sannan wadanda suka kasa zuwa kare kansu aka cire sunayen nasu daga cikin wadanda ke karbar albashi. Ya ce, wannan ne ya sa a kullum suke nanata cewa an yi wannan abu ne don kawo gyara, amma ba wai don muzguna wa wani ko a ci zarafin wani, ko a raba wani da abincinsa ba.

Kakakin Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa, duk wadanda wannan abu ya shafa, an bi duk ka’idojin da suka wajaba wajen sauke su daga aiki, inda wasu ma ba raba su da aikin aka yi ba, an duba ne aka ga suna da takardun shaida na Malanta, don haka sai aka tura su Hukumar SUBEB don a gwada su, sannan daga bisani a turasu makarantun jihar domin koyarwa. “Don haka muna kira ga jama’a kar su bari a rude su, an yi wannan ne don a samu kawo gyara, amma ba wai korar ma’aikata aka yi ba,” in ji Sa’adu.

Da yake amsa wata tambaya cewa, dayake akwai irin wadannan ma’aikata a kusan duk ma’aikatun da ke jihar, ko abin zai kai ga sauran ma’aikatun? Kakakin na Gwamna El-rufai ya bayyana cewa lallai akwai yiwuwar abin ya kai ga kowace ma’aikata, domin ai shi gyara, duk da ba shi da dadi, ana yinsa ne a ko’ina don a samu sauke nauyin al’umma, musamman idan aka yi la’akri da cewa kusan duk kudaden da ake da su suna tafiya ne a albarshi, alhali bai kamata ya zama haka ba.

Ya ce, ai su ma’aikata kadan ne daga cikin al’umma, don haka ba yadda za a yi a ce kudaden da ya kamata a gudanar wa da al’umma ayyuka, ya zama sun tsaya a ma’aikata kadai, “su sauran jama’a ba su da hakkin a yi masu ayyukan ci gaba a inda suke?” Ya tambaya.

Don haka ya ce, shi dama gyara, ko canji a duk inda suke abubuwa ne da ke da wahalar gaske, amma abubuwa ne masu amfani ga al’umma. Don haka jama’a su sani wannan abu da ake yi don neman gyara ne, wanda nan ba da jimawa ba za a fara girbar alhairan da ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here