• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙaruwar Hare-haren ‘Yan Bindiga: Gwamnan Zamfara Ya Gana Da Shugaban Ƙasa

by Leadership Hausa
2 years ago
yan bindiga

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu domin tattaunawa kan yadda ake samun ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga da matsalolin tsaro a jihar.

An yi ganawar ce a ranar Talata cikin sirri a ofishin shugaban ƙasa da ke fadar Aso Rock Villa, Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa Gwamnan ya yi wa Shugaba Tinubu bayani kan ƙaruwar matsalar tsaro a Zamfara, musamman yadda ake ci gaba da kai hare-hare a wasu yankuna.

A cewar sanarwar, shugaba Tinubu da Gwamnan sun tattauna dabaru da matakai daban-daban na shawo kan matsalar tsaro da suka haɗa da ƙara yawan jami’an tsaro, tattara bayanan sirri da kuma shirye-shiryen haɗa kai da al’umma.

  • Abin da muka tattauna da Shugaba Tinubu kan sha’anin tsaron Zamfara – Gwamnan Jihar Zamfara
    https://youtu.be/F-sMeKX9VM4

Ganawar ya kuma bayyana buƙatar magance matsalolin da suka addabi jihar, kamar talauci da rashin aikin yi, waɗanda suke zama silar yawaitar aikata miyagun laifuka a jihar.

LABARAI MASU NASABA

Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Wani ɓangare na sanarwar ta ce: “A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi matsalar tsaro a Jihar Zamfara”.

“A yayin ganawar sirrin, Gwamna Lawal ya sanar da shugaban ƙasa cewa, a cikin shekaru 13 da suka gabata, jihar Zamfara ta zama cibiyar ’yan bindiga a Arewa maso Yammacin Nijeriya.”

“Gwamnan ya roƙi shugaba Tinubu da ya shiga tsakani wajen kawo isassun sojoji, makamai, da kuma kayan aiki, domin ba su isa ba a Zamfara. Ya kuma buƙaci isassun tallafi ta sama don taimaka wa sojojin ƙasa,” in ji sanarwar.

Ta ce, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa gwamnan tabbacin ba da duk wani muhimmin tallafi da dabaru ga jami’an tsaro domin tabbatar da maido da zaman lafiya a Zamfara.”

Sanarwar ta ce, “Bugu da ƙari, shugaban ƙasar ya sake jaddada matsayin gwamnatin sa na ƙin yin sulhu da ’yan bindiga da kuma biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane, matakin da ya yi imanin zai ƙara musu ƙwarin gwiwa ne kawai.”

  • Gwamnan Zamfara Ya Yi Kira A Kara Yawan Sojoji A Jihar Don Yaki Da ‘Yan Bindiga
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe
Labarai

Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe

October 24, 2025
Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi
Labarai

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

October 24, 2025
Next Post
boao

Ana Sa Ran Dandalin Boao Na Bana Zai Hallara Mutane Kimanin 2,000

LABARAI MASU NASABA

Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe

Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe

October 24, 2025
Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu

Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu

October 24, 2025
Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

October 24, 2025
Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

October 24, 2025

Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Sheriff Oboreɓwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma

October 24, 2025
An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya

An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya

October 24, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu

Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.