Ƙungiyar masu wasan dambe ta “Dambe Warriors” ta ƙudiri aniyar ganin an sake fasalin harkar dambe zuwa ta zamani don sana’ar ta zama mai kawo rufin asiri mai yawa.
Shugaban kungiyar, Alhaji Aminu Bature ne ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Otal ɗin CACID dake Kano domin bayyana wa duniya irin kyakkyawan shirin da suka yi don gudanar da wasan dambe a Kano cikin mako mai zuwa a filin wasa na Kano Pillars da ke Sabon Gari.
Shugaban ya bayanna cewa a baya ‘yan Dambe suna yi ne kawai a matsayin al’adar Hausa, amma ba don samun wani rufin asiri ba.
“Saboda haka yace yanzu tun da Allah ya sa muka kafa wannan kungiyar kowa ya ga irin nasarar da aka samu, wanda yanzu haka mun je jihohi da yawa na kasar nan da ma makwabta.
“Na shafe sama da shekara 20 ina yayin dambe, saboda haka na san farin sa da bakinsa, wannan ta sa aka zabe ni a matsayin shugaban kungiyar Dambe Warriors kuma muka tsara sake fasalin Dambe domin tafiya daidai da zamani, sannan kuma a baya dan dambe dan abinda yake samu bai taka kara ya karya ba.
“Yanzu haka muna da rukunin ‘yan damben da suke daukar albashin Naira dubu 370,000.00 ga matsakaita girma da kuma masu ɗaukar Naira 570,000.00 duk wata, sannan kuma wasan damben da ake shirin gudanar da zagaye na karshe a Kano nan ba da jimawa ba duk wanda ya samu Nasara zai yi hafzi da Naira Miliyan guda yayin da sauran za su samu Naira dubu 500,000.
“Sannan kuma a wannan karon za a gudanar da wasan zagayen ƙarshe tare da guda cikin ‘yan damben kasar Saudiyya wanda tuni ya iso muna gudanar da tsare-tsaren da suka rage.” In ji shi.
A karshe shugaban ya jinjina wa abokan aikinsa na dambe tare da yaba wa mai martaba Sarkin Kano wanda shi da kansa ya bayar da kofin da ake sa ran lashewa a lokacin wasan karshe.
Cikin ‘yawan ‘yan damben da za su fafata sun hada da Autan Ali Kanen Bello, Bahago Zayyanu, Dogo Sissco, Hussein ɗan Ƙasar Saudiyya da Sauran ‘yan wasa.