Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya roƙi ‘yan Arewa da su yarda da shi, yana mai tabbatar da cewa yankin zai yi murna da shugabancinsa idan aka zaɓe sa a 2027.
Yayin wata hira da tashar Channels TV a shirin ‘Sunday Politics’, Obi ya bayyana cewa Arewa ce babban arziƙin Nijeriya saboda ɗimbin filayenta da ba a noma ba da kuma tarihin masana’antunta—duka ya yi alƙawarin farfaɗo da su idan ya zama shugaban ƙasa.
- Shirin Tinubu Kan Kiwon Dabbobi Zai Samar Da Ayyukan Yi Miliyan 5 Ga Matasa – Jega
- Dalilin Kwararru Na Bukatar Kafa Cibiyoyin Bincike Kan Nau’ikan Dabbobi A Nijeriya
Obi ya ce matsalolin tsaro da suka addabi wasu sassan Arewa ba za su gagare shi ba. Ya sha alwashin ɗaukar mataki kai tsaye don daƙile ta’addanci da rashin tsaro da ke addabar yankin. A cewarsa, sake dawo da zaman lafiya da farfaɗo da tattalin arziƙin Arewa na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa gaba ɗaya. “Idan na zama shugaban ƙasa, Arewa za ta yi murna. Na fahimci matsalarsu,” in ji shi.
Ya kuma tuna da lokacin da Arewa musamman Kano ke taka rawa a masana’antu da kasuwanci. Obi ya ce Kano na da tarihin masana’antu kamar Bompai, Sharada 1 da Sharada 2, waɗanda a cewarsa za su iya komawa kamar yadda suka kasance. Obi ya bayyana cewa yana da hangen nesa da dabaru da za su inganta tattalin arziƙi da zaman lafiya a Arewa, yana mai jan hankalin yankin da ya ba shi dama domin ya cika waɗannan manufofi.
A ƙarshe, ya sake jaddada buƙatar Nijeriya da ta rungumi sabbin hanyoyi na farfaɗo da tattalin arziki da samar da shugabanni masu gaskiya da jajircewa, yana mai cewa Arewa na da duk abin da ake buƙata domin farfaɗo da ƙasa idan aka tafiyar da albarkatunta da gaskiya da hangen nesa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp