Aƙalla mutane 20 sun rasa rayukansu yayin da wasu gidaje da dama suka kone sakamakon wani mummunan hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin Jebu, da ke Tahos na Ƙaramar Hukumar Riyom a Jihar Filato.
Wasu majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka garin ne a daren ranar Litinin, inda suka fara harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya sa wasu suka jikkata tare da samun raunuka wanda ake ci gaba da kula da su a asibitoci daban-daban.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum 22 Kan Zargin Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka ‘Yan Sa-kai Sama Da 70 A Filato
Shugaba ƙungiyar kare dimokuraɗiyya (COPDEM), Gideon Manjal, cikin wata sanarwa sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne misalin ƙarfe 11 na dare, inda suka shiga gida-gida suna kashe mutane, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da mata da yara da tsofaffi.
Ƙungiyar ta bayyana riƙo ga Shugaba Bola Tinubu, da Mai Ba Da Shawara Kan Tsaron Ƙasa da su ɗauki matakin gaggawa don tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda da ke barazana ga zaman lafiya a Jihar Filato.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’an tsaro game da harin amma ba a samu nasara ba a har zuwa lokacin da ake kammala hada wannan rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp