Biyo bayan hare-haren Sojoji masu tsanani da dakarun haɗin gwiwar atisayen Fansar Yamma suka gudanar, shugabannin ƴan bindiga Abu Radde da Umar Black da ke aiki a ƙananan hukumomin Batsari da Safana a Jihar Katsina sun mika makamansu da kuma fursunonin da suke tsare da su.
Yayin taron miƙa wuyan da aka gudanar a ranar 19 ga Janairu, 2025, a Batsari, an samu halartar duk masu ruwa da tsaki, ciki har da wakilan Sojoji don tabbatar da gaskiya. Ƴan bindigar sun miƙa bindigogi kirar AK47 guda huɗu da fursunoni 15, waɗanda suka haɗa da maza uku, mata takwas, da yara huɗu.
- Turji Na Neman Hanyar Tsira Yayin Da Sojoji Suka Farmaki Mayaƙansa Tare Da Harbe Ɗansa
- Sojojin Sin Sun Gudanar Da Sintirin Hadin Gwiwa Na Shirin Ko Ta Kwana A Tekun Kudancin Kasar
An jaddada cewa wannan ba wata yarjejeniya ko zaman sulhu ba, sai dai wani muhimmin mataki na kai wa ga cikakken miƙa makamai da kuɓutar da duk waɗanda aka sace. An ajiye makamansu a hannun sansanin tsaro na 17, yayin da aka mika waɗanda aka kuɓutar ga ƙananan hukumomi domin gyaran rayuwa da tallafi.