A kokarin ganin an lalubo hanyar magance matsalar rashin tsaro Arewacin kasar wanda ya yi kaka gida, sama da jami’an tsaron daji (NFSS) dubu daya sun bayyana cikakken kudirinsu na fatattakar ’yan ta’adda daga dazukan da ke jihohin Katsina, Kano, Jigawa, Zamfara da Kebbi da Kaduna da kuma Neja wadanda suke fama da matsalolin tsaro.
A wani atisaye na musamman da suka gudanar a Jihar Kaduna domin kara inganta shirin yaki da matsalar tsaro a yankin wanda ya samu halarcin kwamadoji manya da kanana na jami’an daga jihohi bakwai na Arewa maso yammacin kasar nan sunce lokaci ya yi da za su fatattaki duk wani dan ta’adda da ya addabj yankin.
- Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro
- Gwamnati Ta Yaƙi Talauci, Rashin Tsaro, ’Yancin Jama’a Don A Hana Aukuwar Juyin Mulki A Nijeriya – Falana
Atisayen, wanda ya gudana a lwalejin horas da kananan jami’an ‘Yan sanda ya zama na musamman a arewacin kasar, ya hado kwararrun jami’ai daga sassa daban-daban ciki har da masu horar da dakaru, masu leken asiri, da jami’an dabarun yaki da ta’addanci.
Wakilinmi da ya halarci atisayen na Kwana uku ya ruwaito cewa manufar atisayen ita ce kara kuzari da inganta tsari, da tabbatar da cikakkiyar shiri na jami’an da za su shiga dazukan da ke zama mafakar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane dake yankin na Arewa.
Shugaban atisayen, ya bayyana cewa wannan horo na musamman yana cikin matakan da ake dauka domin yin amfani sabbin dabaru da fasahohi da za su ba jami’an ikon gudanar da bincike mai zurfi, gano maboyar ’yan ta’adda, da kuma kai farmaki ba tare da jinkiri ba.
Da yake zantawa sa wakilinmu jim kadan bayan Kamala atisayen, mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Tsaron Daji na kasa (NFSS) mai kula da Ayyuka, Manjo Muhammad Abubakar Abdullahi mai nurabus, ya ce hukumar na kara samun kaimi wajen amfani da sabbin dabaru da tsare-tsare don kare dazukan kasar.
DCG Mohammed, ya bayyana suna gudanar da irin wannan atisayen musamman duk karshen shekara na Arewa maso yamma bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da ingantaccen tsaro a dazukan Nijeriya.
Ya bayyana cewa NFSS za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro domin lalata maboyar ’yan bindiga da sauran miyagu da ke cikin dazukan kasar.
DCG Mohammed ya bayyana cewa bayan kammala atisayen, za a tura dakaru daban-daban zuwa muhimman dazuka da ake fuskantar barazana domin karfafa hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da cewa Najeriya ta samu zaman lafiya mai dorewa.
Ya ce: “Mun tara wadannan jami’ai ne domin tabbatar da cewa kowannensu ya samu cikakken horo da kuma fahimtar dabarun aiki a daji, kuma samu kayan aiki na zamani da za su ba su damar cin nasara a kowanne fanni.”
Wani jami’in leken asiri na hukumar ya bayyana cewa horon ya kunshi koyon yadda ake shige da ficen dazuka da dabarun gano layukkan sadarwar ’yan ta’adda, da kuma hanyoyin katse su ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Shugaban Sashen Leken Asiri na Arewa maso Yamma, Habibu Shehu Yakawada, ya ce jami’an hukumar sun shirya tsaf wajen amfani da gogewa da kwarewarsu a matsayin tsofaffi da masu aikin tsaro domin inganta tsaron daji.
Ya kara da cewa hukumar na da jami’ai a fadin kasar kuma za ta ci gaba da aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin samun dawwamammen sakamako.
A nasa jawabin,Wakilin Shugaban karamar Hukumar Nassarawa da ke Jihar Kano, Sani Jibrin SK Tudun Murtala wanda ya wakilci gwamnatin Jihar Kano, ya tabbatar da ci gaba da bayar da goyon baya ta fannoni daban-daban. Ya bayyana tsaro a matsayin alhakin kowa, tare da nanata kudirin Gwamnatin Jihar Kano na kare rayuka da dukiyoyi, yana kuma jinjina wa jami’an tsaro.
Kwamandan NFSS na Jihar Kano, Abdullahi Al’amin, ya ce wannan shi ne karo na 15 da ake gudanar da irin wannan horo, yana mai kara da cewa ba da jimawa ba za su fito fili su nuna shirinsu ga ’yan kasa a matsayin hanyar karfafa amincewar jama’a ga hukumar NFSS.
Ya tabbatar da cewa hukumar na da cikakken niyyar kawar da ’yan bindiga da sauran miyagun mutane daga dazuka da sauran yankunan kasar.
Shima Shugaban Sashen Fasaha da kirkire-kirkire na hukumar ta (NFSS) DCG Y. A. Abdulkareem, ya ce hukumar za ta yi amfani da sabbin hanyoyin tattara bayanan leken asiri da fasahohi sadarwa don inganta ayyuka da karfafa tsaron dazuka a fadin Nijeriya.
Haka zalika, an gudanar da atisayen kai farmaki na karshe, inda jami’an suka nuna kwarewarsu ta yadda za su kewaye daji, su toshe hanyoyin tserewa, sannan su fatattaki duk wata kungiya ta miyagu da ke cikin yankin.
Wani jami’i daga cikin mahalarta atisayen ya ce: “Mun dauki wannan horo da muhimmanci domin kare rayukan ’yan kasa. Za mu shiga dazuka ba tare da tsoro ba har sai mun kawar da barazanar ta’addanci.”
Da yawan jami’an tsaron dajin da suka zanta da wakilinmu sun tabbatar da cewa jama’ar yankunan arewa sun nuna gamsuwa da wannan mataki, suna masu fatan cewa sabon shirin zai kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta dade tana addabar su.














