Rundunar ’Yansanda ta Jihar Gombe ta bayyana wasu laifuka da ta kama masu aikatawa tare da gurfanar da su ga kafafen yada labarai, bisa jagorancin DSP Buhari Abdullahi a madadin Kwamishinan ’Yansanda, CP Hayatu Usman.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani gungun masu satar shanu da suka haɗa da Mohammed Garba da wasu mutum uku, waɗanda suka shiga hannu bayan an kama su suna ɗaukar shanu daga wani ƙauye a Kumo, ƙaramar hukumar Akko. Haka kuma, an kama wasu samari masu suna Uzaifa Umar da Isa Ibrahim a Barunde kan ɗaukar makamai da nufin tada hankali, inda aka same su da wuƙa da adda.
- SIMDA Ta Ƙulla Alaƙa Da Jami’ar Skyline Kan Ci Gaban Ilimi Da Kasuwancin Zamani A Kano
- Gombe Ta Kafa Tarihi Na Amincewa Da Dokar Kare Masu Bukata Ta Musamman
A wanin lamari daban, ’yansandan sun kama mutane shida da ake zargi da shiga gidan wani a garin Bagadazan, suka yi awon gaba da kudi sama da Naira miliyan uku da babur. Haka kuma, an kama wasu matasa masu shekaru 16 zuwa 18 da laifin kashe wani yayin da ake shagalin biki a Jauro Ali.
Kwamishinan ’Yansanda ya yaba wa jami’an da suka yi kokari a gurfanar da masu laifuka, ya kuma jaddada ƙudirin rundunar na ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.