Rundunar Ƴansanda ta Jihar Kano ta kama wasu mutane uku da ake zargi da satar motoci da safararsu zuwa ƙasashen waje, bayan da suka saci mota a wani kamfanin sayar da motoci yayin gwajin tuki.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa wanda ake zargi da jagorantar ƙungiyar ɓarayin mai suna Shamsu Yusuf da ake kira “Chitta” an cafke shi tare da abokan aikinsa guda biyu bayan wani aiki na musamman da jami’an Special Intervention Squad (SIS) suka ƙaddamar.
- Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu
- Rundunar Ƴansanda Ta Gayyaci Jami’anta Da Bidiyonsu Ya Yaɗu Suna Karɓar Cin Hancin Naira 5000
An kama su ne bayan wani rahoto daga dillalin mota, Abdulqadir Abdurrahman na unguwar Gadan Ƙaya a ranar 7 ga Yuli, inda ya bayyana cewa Chitta ya zo Dangari Motors yana nuna sha’awar sayen mota, amma sai ya tsere da wata Toyota Corolla ƙirar 2013 mai launin zinariya yayin gwajin tuƙi.
Bincike ya gano cewa motar an riga an saida ta a Jamhuriyar Nijar, kuma an gano ta bayan cafke Bashir Ladan daga Katsina da Suleiman Muntari daga Tudun Matawalle, Katsina. Wanda ake zargi da jagorancin su ya amsa laifin satar motoci da dama ciki har da Mercedes Benz GLK.
Kwamishinan Ƴansanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da jajircewar jami’an sannan ya buƙaci masu dillancin motoci da su ƙara lura da kwastomominsu, yana mai tabbatar wa da al’umma da cewa rundunar na kan tsayin daka wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp