Ƴansandan Jihar Kano sun cafke ɗalibai 11 daga Makarantar Kwalejin Gwamnati ta Bichi bisa zargin hannu a kisan wasu ɗalibai guda biyu a makarantar kwana.
Mai magana da yawun rundunar, SP Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kama ɗaliban a yau Alhamis, inda ya bayyana cewa an kama su ne domin gudanar da bincike da kuma gano irin rawar da kowanne ya taka.
- Kano Pillars Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Gidan Rediyon RFI Hausa
- An Fara Binciken Mutuwar Wasu Ɗalibai 2 A Makarantar Kwana A Kano
Ya ce, “An kama ɗalibai guda goma sha ɗaya dangane da lamarin, kuma ana ci gaba da bincike don tantance irin rawar da kowanne daga cikinsu ya taka.”
SP Kiyawa ya kuma tabbatar da cewa ƴansanda za su yi duk mai yiwuwa don gano gaskiya da tabbatar da cewa duk wanda aka same shi da laifi an gurfanar da shi gaban shari’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp