Rundunar ‘yansanda ta jihar Filato ta kama mutum 859, ta kwato makamai 27 da alburusai 115 a shekarar 2024, kamar yadda Kwamishinan yansanda na jihar, Mista Emmanuel Adesina, ya bayyana a taron manema labarai a Jos a jiya Juma’a.
- ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Makiyaya Tare Da Kashe Shanu A Jihar Filato
- Sojoji Sun Kama Mutane 20 Kan Zargin Kashe-kashe A Jihar Filato
Adesina ya ce rundunar ta ceto mutum 46 da aka yi garkuwa da su tare da gurfanar da mutum 415 a kotu bayan kammala bincike. Ya ce wannan nasara ta biyo bayan dabarun da aka bi don hana aikata laifuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.
Ya kuma gode wa gwamnatin Filato da al’ummar jihar bisa goyon baya da suka ba rundunar, musamman a fannin bayar da bayanan sirri da suka taimaka wajen nasarorin da aka samu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp