Rundunar Ƴansanda ta Jihar Sakkwato ta kama mutum uku da ake zargin su mambobi ne na wata shahararriyar ƙungiyar Sai Malam yayin wani aiki da Sashen Yaƙi da Satar Mutane na Rundunar ya gudanar a ranar Jumma’a.
An kama su ne n sakamakon nuna damuwar jama’a game da yawaitar ayyukan wannan ƙungiya a faɗin jihar.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Ahmad Rufai, ya fitar, babban wanda ake zargi, Usman Shu’aibu, da wasu biyu suna hannun ƴansanda kuma “tun daga lokacin sun bayar da cikakken bayani game da ayyukan ƙungiyar.”
- An Ɗauke Nnamdi Kanu Daga Gidan Yarin Abuja Zuwa Sakkwato
- Gwamna Otti Ya Ziyarci Nnamdi Kanu A Gidan Yarin Sakkwato
DSP Rufai ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa ƙungiyar na ɗaukar matasa ba tare da sun sani ba ta hanyar wani dandalin WhatsApp mai zaman kansa da ake kira Red Chamber, wanda ake amfani da shi wajen jawo mutane cikin ayyukan laifi da rashin ɗabi’a.
A cewar ƴansanda, ayyukan ƙungiyar sun haɗa da “sihrin asiri da ayyukan tsafi, neman ƙarfin shaiɗanci, ayyukan batsa na jinsi ɗaya, ta’addanci da tashin hankali da aka tsara.”
Kwamishinan Ƴansanda na Jihar, CP Ahmed Musa, ya tabbatar wa jama’a cewa za a ƙara himma wajen ɗaukar mataki kan wannan ƙungiya da sauran ƙungiyoyin laifi masu kama da su.
“Muna so mu tabbatar wa al’ummar Sakkwato masu kirki cewa muna sauraron damuwarsu. Kama waɗannan mutane da ake zargi shaida ce a fili cewa an amsa kiransu na ɗaukar mataki. Ƙoƙarinmu ya rushe wani muhimmin reshe na wannan ƙungiya mai suna Sai Malam, kuma mun himmatu wajen tabbatar da tsaro da aminci ga kowane ɗan ƙasa,” in ji shi.
Rundunar ta kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su lura sosai da amfani da wayoyin zamani da ayyukan su a kafofin sada zumunta, sannan su hanzarta kai duk wani abin da ke da zargi ko tasirin abokai ga hukumomin tsaro.
Hukumomin ƴansanda sun ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin gano sauran mambobin ƙungiyar, tare da roƙon jama’a da su ci gaba da haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin lokaci.














