Iyayen daliban Nijeriya da suke karatu kasashen waje a karkashin tsarin tallafin karatu na (BEA) sun mika kukansu kan abinda suka kira irin wahalhalun da ‘ya’yansu ke fuskanta, saboda halin da gwamnatin tarayya ta yi na ko in kula wajen rashin basu kudaden tallafi har abin ya kai ga ku san shekara uku.
Da yake jawabi ranar Litinin ta wannan makon da muke ciki mai magana da yawun kungiyar, BEA’, Mrista Abang Matthew, ya bayyana ywancin masu karatu a kasashen Turai , Asiyia, Arewacin Afirka, da sauran kasashe abokan tafiyar yanzu suna cikin yunwa,babu wurin kwana, sannan kuma basu cikin walwala,saboda gwamnati bata cika alkawurran da tayi masu ba.
Ya ce shekarar 2025 ita ce shekarar da daliban suka fi shan wahala, domin ya yi bayanin babu ko sisin kwabon da aka ba wani dalibi tun farkon wannan shekarar, wanda hakan yasa suka kammala shekarar karatun cikin kunci ba tare da wani taimako ba.Ya tuna da cewa a shekarar 2024, daga cikin dala $500 zuwa $220, dan kudin da yace ba zai iya biyan ko bukatun da suka zama dole ba, wato kamar abinci,dakin kwana,kudade zurga- zurga, na kulawa da lafiya, hakanan ma a shekara 2023, ba a basu na wata biyu ba, tare da na wata hudu suma dai ba’a basu ba.
Lokacin da jaridar leadership ta tuntube shi darektan mai kula da lamurran ‘yan jaridu na ma’aikatar kudi ta tarayya, Mista Mohammed Manga, domin asan daliln da yasa aka samu daukar lokaci ba’a biya ba yaki amsa kiran da aka yi ma shi ta wayar shi, da kuma sakunan da aka aika.
Wasu daga cikin iyayen da suka yi hira da ‘yan jaridu lokacin zanga- zangar, sun ce dogon lokacin da aka dauka ba tare da biyan kudin ba karamar wahala ‘ya’yansu dake karatu a kasashen waje suka sha ba.
Sun bayyana rasuwar wani dalibin Nijeriya, Bashir Malami, da yake yin karatu a kasar Morocco, abinda suka ce wata kaddara ce da za a iya maganinta.Kamar yadda suka jaddada, Malami ya kasa samun kulawar asibiti ta gaggawa ne saboda rashin kudi, halin da ya ga laifin gwamnati wajen gazawar da tayi ta biya su ‘yan kudaden da suka dogara kansu.
Daltatu Tijani ya ce yawancin daliban yanzu basu da lafiya, ga kuma yawan damuwa, suna kokarin yadda za su tafiyar da rayuwa a kasashen waje inda suke da tsauraran dokoki na shige da fici da kuma tsadar rayuwa.
Anan gida, Iyayensu na sayar da kaddarori suna amsar bashiin Bankuna, da kuma samun rance daga wurin ma kwabta domin su taimakawa ‘ya’yansu wadanda gwamnati ce ya kamata ta dauki nauyinsu.
“Mun, zo nan ne domin mu kara tunatar da gwamnati ta dube mu da idon rahama a matsayinmu na ‘yan Nijeriya, wadanda daliban suka iyakar kokarinsu Allah ya basu basira, domin sune Shugabannin watarana, yayin da suke a kasashen waje, suna mutuwa da kuma kuka, bugu da kari kuma ga yunwa, da kuncin rayuwa, hakanan gidajen da suke haya masu gidajen suna matsa masu da sauran abokan tafiya,”kamar daya daga cikin Iyayen, Mbashall Grace ta bayyana.
Wani dalibi, Aliyu Aliyu Alkali, ya ce Iyaye da su dalibai sun rubuta wasiku, sakon kar ta kwana, sun ziyarci ma’aikatu, da kuma wasu hukumomi da suka hada da, NIDCOM, hukumar bada tallafin karatu ta tarayya, ma’aikatar kudi, da kuma majalisar kasa amma har yanzu babu wani abinda zai nuna da akwai nasara a gaba.
Ya yi kira da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, sai kuma Ministocin ilimi da kudi, mambobin majalisun kasa da su kawo dauki ba tare da bata lokaci ba.Ya ce daliban ba suna neman wani abin jin dadi bane, amma suna bukatar kawai gwamnati ta biya su kamar yadda ta yi masu alkawari aka kuma sa lamarin cikin kasafin kudi.
Iyayen sun yi kira da a biya daliban ragowar kudaden da suke bi, da kuma komawa biyan dala $500 kowane wata, a kuma rika biya da gaskiya, a bada taimako na lamarin wurin kwana, sai kuma maganar kula da jin dadi inda abin ya zama dole, da lura da irin halin da suke, domin a samu kare daliban Nijeriya da suke karatu a waje.
Matthew kira da ‘yan Nijeriya, kungiyoyi masu zaman kansu, sai kuma kafafen yada labarai cewar su bada tasu gudunmawa domin a dauki mataki, saboda abin bana siyasa bane, amma maganar jinkai ce da kuma tausayi wanda yake damuwar ‘yan makaranta bwadanda sune jagororin wata rana.Ya yi kira da gwamnatin tarayya idan bata yi abinda ya kamata ba cikin lokaci, za’a samun karin daliban da za su bar makaranta ko kuma su rasa rayuwarsu.
Rashin Dakunan Kwana, Lalacewar Abubuwa Ke Sa Dalibai Nema A Waje
A fadin makarantun Nijeriya, babu wadda ba ‘a fafutukar neman dakunan kwana ana ci gaba da yin hakan duk kuwa da yake gwamnati tana bada tata gudunmawar.
Yawancin wuraren da dalibai suke kwana, LEADERSHIP tana da masaniyar cewa lamarin neman wuraren kwana a manyan makarantu wadanda suke nema sun fi wuraren kwanan da ake da su yawa, hakan ke sa ana barin dubban dalibai su shiga neman wuraren da za su rika kwana ba kuma cikin makaranta ba.
Karuwar yawan dalibai, da kuma lamarin kayan da suka tsufa saboda dadewar da suka yi, da kuma yadda samar da abubuwan more rayuwa yake tafiyar Hawainiya,abinda shi ne ya kara dagula matsalar kamar dai yadda binciken da aka yi ya nuna.
Ga wadanda suka yi sa’ar samun wurin kwana a makaranta,da akwai dai maganar cunkoson daki, lalacewar abubuwa,rashin ingantattar wutar lantarki, ga kuma rashin tsafta, wadannan abubuwa sune suke karawa su daliban shiga halin ya – nika- yi.
Ga sauran, karin matsalolin na kwana ba cikin makaranta ba suna da yawa-cdomin zama irin wadandacan wuraren na iya kusantar dasu ga hanyoyin da za’a rika dugunzuma masu, rashin tsaro,yin tafiya mai nisa wajen zuwa da dawowa daga makaranta ko shakka babu abin zai shafi karatu.
Duk da yake gwamnatocin Tarayya da Jihohi, har ma da Jami’oi masu zaman kansu, sun yi alkawari na maganin matsalar, dalibai a wuraren kwanansu daban daban sun bayyana wa LEADERSHIP har yanzu irin matsalar tanan bata canza zane ba.
Wadannan daliban sun nuna irin matsalolin da suke fuskanta, gajiya, da karin samun karuwa ta yadda dalibai suke sfuskantar wahala kan yadda suke neman wuraren kwana a manyan makarantu.
Zama ba a cikin makaranta ba akwai matsala cewar Kana
A Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi,Hauwa Shau’aibu Kana, ita ma tana daga cikin masu fuskantar irin wadannan matsalolin.Ta bayyana yadda rashin wurin kwana yasa take kwana wurin da yake nesa daga makaranta, irin hatsarorin da take fuskanta kamar yadda tace suna da yawa.
“Babu wuraren da za’a ajiye gado, don haka akwai matslar samun dakin kwana a lokaci na farko.Wuraren kwanan da ba’a makaranta suke ba suna da tsada da akwai kuma wuyar a same su.Ni ina zama a wurin da yake da nisa, shi yasa idan ina da laccar da za’a yi da wuri, ba kasafai nake samu ba.”
Da akwai ma maganar tsaro na cikin abinda ya dame ta. “Za ka ji maganar ana yin sata da kuma rashin tsaro musamman ga wadanda suke kwana ba a ciukin makaranta ba, amma da akwai matukara wuya ka samu irin wadancan matsalolin idana aka ce kana zama cikin makaranta.A cikin babu wata babbar matsala da akwai tsaro.
“Makarantar ya dace ta kara gina dakunan kwana na dalibai domin hakan zai sa kowane dalibi ya samu wurin da zai kwana.Hakanzai rage rashin tsaro da kuma taimakawa wajen samun damar shiga lacca kan lokaci, a samu damar da za’a maida hankali kan karatu daga karshe a fita da sakamako maikyau kamar yadda ta bada shawara,”.
Victor Ya ce su 8 suke kwanciya kan gado 4
A Jami’ar Bingham, Bictor Patrick, dalibi mai karanta aikin jarida, Jami’ar Bingham ya ce duk da yake sabbin wuraren kwanan dalibai wadanda ake ginawa har yanzu suna fuskantar matsalar.
“Suna da yawa kamar yadda yace, wuraren da suke kowane daki ba za su ishe mu ba, duk kuwa da yake makaranta ta gina sabbin dakunan kwana 20, sai dai har yanzu basu ishe su ba kama yadda ya jaddada,’’.
Yawan kudin hayar dakuna, rashin ruwa ya sa rayuwa ta tsauwala cewar-Adams
Shi kuma Toyeebah Yabodey Adams, dan aji biyu, a Jami’ar Confluence,Osara da yake shi ba cikin makaranta yake kwana ba shi matsalolin nasa sun hada da tsauwalar rayuwa saboda tattalin arziki.
Toyeebah ya bayyana yadda dalibai suke fuskantar karin kudin haya da kuma rashin ruwa a gidajen da ban a makaranta ba ne.
Mufida ta ce su ne a daki, akwai cunkoso amma dai akwai tsaro
Ita kuwa Mufidat, ‘yar aji 4 ta Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, da ke Lapai, cewa ta yi rayuwa a cikin Jami’a wata irin dama ce da kuma yadda mutum zai koyi tafoyar da rayuwarsa da babu dadi ga ita rayuwar.
Tana zama cikin makaranta sai dai kuma rayuwar sai dai kawai ayi sha’ani, ana dai zaman rayuwa ce irin ta makaranta.














