An ruwaito cewa wani dalibin Makarantar Lauyoyi ta Nijeriya Ayomiposi Ojajuni, ya kashe kansa bayan an hana shi rubuta jarabawar karshe ta Bar Final a sansanin Yola, Jihar Adamawa.
PUNCH Metro ta samu labarin daga akalla dalibai biyu da suka san lamarin, wadanda suka yi magana karkashin sharadi na boye sunansu saboda yadda al’amarin ya ke da sarkakiya, cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar.
An ce Ojajuni, wanda ya kammala karatunsa a Olabisi Onabanjo Unibersity, an yi masa jerin tambayoyi daga shugabannin makarantar, daga bisani kuma aka gano cewa ba za a ba shi damar halartar jarabawar kwararru ba, wadda ta fara a ranar daya.
Wani dalibi a makarantar lauya da ya yi magana da wakilinmu a ranar Lahadi cewa, “An yi masa tambayoyi a baya. Ko da ba mu san cikakken abin tambayoyin ba, daga baya ya gano cewa ba za a ba shi damar shiga jarabawar ba. Wannan ne ya sa ya shiga damuwa sosai, kuma hakan ne ya jawo mutuwarsa.”
Wani dalibi a makarantar ya ce Ojajuni ya rasu ne bayan shan wata guba.
“Ya sha wani abu mai hadari a ranar Asabar kuma ya rasu a ranar Lahadi bayan an kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama, Yola,” in ji shi.
Lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Adamawa, Yahaya Suleiman, a ranar Lahadi, ya ce, “Ba a ba ni izinin yin sharhi kan wani aikin jarabawa na hukuma ba. Ina Abuja.
Na dai karanta labarin ne a jarida kamar yadda ku kuka karanta.”
A halin da ake ciki, wata kafar labarai ta Intanet, FactCheckNews, ta ruwaito a ranar Lahadi cewa Ojajuni ya kashe kansa ne bayan kasa cika kashi 75 cikin 100 na halartar darussa da ake bukata domin cancantar shiga jarabawa.
“Majiyoyi a sansanin makarantar sun shaida wa wakilinmu cewa a baya, sunan wadanda suka cancanci shiga jarabawa kan fito makonni biyu kafin jarabawar, wanda hakan ke ba wa dalibai da ba su kai kashi 75 cikin 100 ba bisa dalilan lafiya na gaskiya damar gyara matsalarsu.
“Amma a kwanan nan, makarantar ta dauki sabon tsari na sanya sunayen ne a karshe kafin jarabawa, ba tare da barin wani lokaci don gyara irin wadannan halaye ba.”
- NDLEA Ta Kama Kilo 588 Na Miyagun Ƙwayoyi, Ta Ƙona Hekta 6 Na Gonakin Wiwi A Adamawa
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Uku Bayan Rufe Makarantu A Adamawa
“Bayan ganin cewa bai cancanci shiga jarabawar ba, dalibin ya sha wani abu da ake kyautata zaton gubar bera ce, wanda hakan ya jawo masa rashin lafiya mai tsanani har ya rasu,” in ji kafar labaran.
Lokacin da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan Sanda na Jihar, Suleiman Nguroje, ya ce har yanzu ba a kai rahoton lamarin gare su ba.
Ya ce, “Har yanzu ba mu sami irin wannan rahoton ba. Na kira DPO a yankin, amma ya ce bai samu rahoton ba. Haka nan na yi kokarin kiran makarantar lauya, amma ban samu nasarar samun su ba.”














