An yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na jihar Katsina da su yi karatun ta nutsu su sake tunani game da ɗaukar ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar Katsina a zaɓen 2023 mai zuwa.
Wani matashi ɗan jami’yyar APC a garin Katsina Sule Dudu Kofar Marusa ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.
Abdulkarim Dauda Daura na ɗaya daga cikin mutane tara da suka shiga zaɓen fidda gwani amma bai samu nasara ba a ƙarƙashin jam’iyar APC a jihar Katsina.
Sule Dudu Kofar Marusa ya ce idan jami’yyar APC ya ɗauki Abdulkarim Dauda Daura a matsayin wanda zai yi wa ɗan takarar jam’iyyar APC mataimaki zai taimaka wajan shawo kan matsalar tsaro.
Ya kuma ƙara da cewa har yanzu wuri bai korewa jami’yyar APC ba kasancewar Abdulkarim Dauda Daura masanin tsaro ne duba da irin yanayin da jihar Katsina ta shiga akan halin rashin tsaro.
“Abdulkarim Dauda Daura masanin tsaro ne, wanda yanzu haka yana ƙasashen waje akan abinda ya shafi sha’anin tsaro a duniya, inda ya ziyarci Kasashen Mexico da France da Italy da sauran su” inji shi.
Matashin dai ya ƙara da cewa idan har Masari da Dikko Umar Raɗɗa da Jami’yyar APC suna son cin zaɓe to su jawo A.D Daura su bashi mataimaki gwamna domin samun nasara a zaɓen 2023.
Haka kuma Sule Dudu ya yi bayanin cewa A.D Daura yana da kyakkyawan tarihi a lokacin da ya yi aikin ɗan Sanda, ba a taɓa kama shi da cin amana ba, sannan ya samawa jama’a da dama aikin yi fiye da mutane dubu biyar (5,000)
Sule Dudu ya ce idan jami’yyar APC ta ɗauki Abdulkarim Dauda Daura mataimakin gwamna za su samu mafita kuma wuri bai kore ba, yana mai cewa hakan zai baiwa yankin Daura mai ƙananan hukumomi 12 kawo kuri’unsu fiye da kashi 75%
“Lallai ya kamata jami’yyar mu ta APC ta san cewa Annabi ya fako, ta sake tunani, ta yi abinda ya kamata, duba da cewa akwai wasu alƙawura da har yanzu bata cika ba, wanda idan ba a yi abinda ya kamata ba, za a yi samun matsala” inji Sule Dudu
Daga karshe ya yi kira ga jama’a da su ajiye siyasa gefe guda akan matsalar tsaro, saboda shi dai ɗan ta’adda baya da gwani kowa ɗauka yake, ba ruwan shi da ɗan APC ko ɗan PDP koma wace irin jami’yya kamawa yake.