ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

12 Ga Yuni: Muhimman Abubuwan Da Buhari Ya Fada A Jawabinsa Na Ranar Dimokuradiyya

by Muhammad
4 years ago
12

Ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara ake bikin zagayowar Ranar Dimukuradiyya a Nijeriya.

An fara gudanar da bikin wannan rana ce tun daga shekarar 2002, haka kuma shugaba Muhammadu Buhari ya kara wa wannan rana karfi a shekarar 2018 bayan da ya sauya Ranar Dimokuradiyyar daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa ranar 12 ga watan Yuni.

  • 12 Ga Yuni: Atiku, Tinubu Da Obi Da Ragowar Wasu Za Su Sanya Furanni A Kabarin Abiola
  • 2023: An Bukaci Tinubu Ya Dora Kan Irin Salon Mulkin Buhari Kwabo Da Kwabo

Aminiya-trust ta wallafa jawabin da shugaba Buhari ya gabatar a safiyar ranar Lahadi, cewa ya soma ne da bayani kan muhimmancin Ranar Dimokuradiyya inda ya jaddada muhimmancin zaben Yunin 1993 a tarihin Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari ya ce kada ’yan Nijeriya su manta da irin gudunmawa da sadaukar da kai da gawarazan dimokuradiyya suka bayar a 1993.

Ya bukaci ’yan Nijeriya da su yi koyi da kishin kasa irin na magabata a duk lokacin da za su zabi shugabanni.

LABARAI MASU NASABA

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Shugaban ya sake tuna wa ’yan Nijeriya cewa wannan ce Ranar Dimokuradiyya ta karshe da zai yi a matsayinsa na Shugaban Kasa inda ya ce yana cike da kudirin tabbatar da cewa an zabi sabon shugaban kasa ta hanyar zabe na gaskiya da adalci.

Haka kuma Shugaba Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani a kasar inda ya ce daya daga cikin abin da ya birge shi da zaben shi ne yadda mata da matasa a kusan duka jam’iyyun suka fito neman takara, “wannan alama ce da ke nuna dimokuradiyyar Nijeriya ta kara bunkasa a cikin shekara 23 da aka shafe.

“Yayin da muke shiga kakar yakin neman zabe da kuma zabe na gama gari, kada mu taba daukansa a matsayin wani alamrari na a mutu ko a yi rai, dole ne mu tuna cewa dimokuradiyya ta yi tanadin abin da mafi rinjayen kaso na alumma suke so, saboda haka dole za a samu masu nasara da masu faduwa.

Shugaban ya bayyana cewa a shekara bakwai da ya shafe kan mulki, gwamnatinsa ta yi kokari wurin gyara Dokokin Zabe da yanayin gudanar da zaben domin kare kuri’un al’umma.

Kan dai batun zaben, Shugaba Buhari ya bayyana cewa bangaren Zartarwa da Dokoki da kuma Shari’a na da kudirin ganin sun aiwatar da wadannan sauye-sauye na Dokokin zabe a yayin zaben 2023.

Shugaba Buhari ya kuma bukaci duk ’yan Nijeriya su saka wadanda rikicin ta’addanci ya rutsa da su cikin addu’a, yana mai cewa a kullum yana kwana yana tashi da bakin cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya bayar da tabbacin cewa duk hukumomin tsaron kasar na yin duk mai yiwuwa domin ceto wadanda aka sace.

“Na san cewa muna cike da damuwa kan yadda ake fama da kalubale na matsalar tsaro a sakamakon ayyukan ta’addanci, a matsayinmu na gwamnati muna aiki tukuru don shawo kan wadannan kalubale.

“Don ganin an samu biyan wannan bukata, dole kowa ya bayar da gudunmawa. Ba aikin gwamnati ba ne ita kadai, akwai bukatar dukkan yan kasa su ba rika bai wa jamian tsaro hadin kai ta hanyar mika musu rahoton duk wani mutum da ake zargi da aikata laifi ko wani motsi da basu yarda da shi ba.

“Zan karkare wannan jawabi na Ranar Dimokuradiyya, wanda kuma shi na karshe da zan yi a matsayina na Shugaban kasa, ta hanyar tabbatar muku da kudirin da na dauka na kare Najeriya da ‘yan Nijeriya daga dukkan makiya daga ciki da waje.”

Buhari ya rufe jawabansa da Yi Wa Nijeriya Addu’a.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN
Labarai

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Next Post
12 Ga Yuni Sam Ba Ta Dace Da Ranar Dimokradiyya Ba A Nijeriya —Ra’ayin Najib Sani

12 Ga Yuni Sam Ba Ta Dace Da Ranar Dimokradiyya Ba A Nijeriya —Ra'ayin Najib Sani

LABARAI MASU NASABA

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025
An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.