Anyi kira ga Gwamnatin Kano karkashin Dokta Abdullahi Umar Ganduje akan ta kara kwazo akan abinda take wajen bunkasa cigaban ilimin addini ta cigaba da baiwa ilimin makarantun Kur’ani dana Islamiyya kulawa sosai.
Daya daga cikin wadanda kungiyar “BATTLERS” ta karrama bisa gudummuwarsa na gina makaranta na sama da N10,000,000 ta Islamiyya a Unguwar Zage ga al’umma, Alhaji Fatihu Idris Usman Dorayi Bayan Asibitin Murtala ya yi kiran da yake zantawa da manema labarai. Ya kuma kara da cewa, a matsayin Gwamna na mai hidimtawa addini ya dada jajircewa wajen taimakawa makarantun Islamiyya saboda sunfi na Boko muhimmanci, Duk da dai sun yi farin ciki da kwamiti daya kafa bisa jagorancin Dokta Tahar Adamu, Kwamishinan addini na duba makarantun Kur’ani da suke sa ran za’a basu kulawa na musamman a jihar Kano.
Alhaji Fatihu Idris Usman ya godewa Allah bisa wannan karramawa da akayi masa tare da jan hankalin al’umma suyi koyi da abubuwa da za su taimakawa cigaban ilimi.Unguwanni su rika hada-kai a rika bude kungiyoyi a rika duba ratuwa na jama’a ana samun hadin-kai a taimakawa juna domin rayuwa a wannan zamani ba za’a yi nasara ba mutukar ba’a hada kai ba dukkan al’umna a taimaki juna wadanda suke da bukata an sansu a hada-kai a taimaka musu.
Alhaji Fatihu ya ce, baiso aka bayyana cewa shiya gina makaranta ba don abu ne ya yi don Allah da taimako aka baiwa Allah da Manzo to kamata ya yi a rufe. Amma tunda an bayyana abinda ya ja hankalinsa shine yara da suke dasu sama da dubu dake karatu kullum akan gada kowane lokaci komai tsananin sanyi da damina da rana wannan tasa ya ci alwashin in Allah ya kawo wani abu a kusa da wajen da za’a samu a gina musu makaranta za’a saya a gina. Allah cikin ikonsa ya kawo wasu gidaje guda biyu a kusada wajen da suke aka saya akayi musu makaranta da suke karatu a ciki yanzu.