Connect with us

NAZARI

Nazarin Kwanaki 330 A Yunkurin Juyin Mulki A Turkiya

Published

on


Daga Rabi’u Abubakar Zariya

Na rubuto muku wannan ne edita domin neman alfarmar yin tsokaci da nazari a kan rikicin yunkurin juyin mulkin kasar Turkiyya, wanda bai yi nasara ba. A kullum kafafen yada labarai a Nijeriya daban-daban su kan yi tsokaci a kan lamarin, wanda a yanzu ya zama abin nazari a duniya baki daya. Ya zuwa yau dai lissafi ya nuna cewa an shafe kwanaki 330 da faruwar lamarin a ranar 15 ga Yulin 2016.

A daidai lokacin da lamarin ya auku gwamnatin kasar bisa jagorancin Shugaba Recep Tayyib Erdogan ta fara tsaurara matakan tsaro gami da neman dukkanin masu hannu a cikin bahallatsar, inda ba a jima ba gwamnati ta fara bayyana fitaccen Malamin nan da a yanzu yake zaman gudun Hijira a kasar Amurka, wato Sheikh Fethullah Gulen da mabiyansa da hannu ciki, musamman ganin yadda gwamnatin kasar ta rika matsa kaimi kansa da mutanen nasa. Mun sha ganin irin wadannan rahotannin, inda shi kansa Shugaba Recep Tayyip Erdoğan na kasar yake fitowa da kausasan kalamai a kan dakile dukkannin masu hannu a cikin yunkurin na juyin mulki.

Me ya kamata mu a nan kasar mu fitar, duk da na karanta wani sharhi da wani malami ya aiko a wannan jaridar da sauran kafafen yada labaran Hausa cewa, idan mun kwatanta da al’amuran da ke faruwa a farfafjiyar siyasar kasar nan tamu ta Nijeriya, sai mu ce irin wannan matsalar tana nan a ko’ina. A kwanan nan, jigo kuma gogarma a jam’iyyar APC mai mulki Cif Bola Ahmed Tinubu shi ma ya fito tare da bayyana ra’ayinsa na yin tir da duk wani yunkurin da sojoji za su yi don juyin mulkin Nijeriya. Ashe ke nan duk inda harkar juyin mulki ta kunno kai, shakka babu da wuya a tsinci hairan a ciki. Duba da yadda al’amura a fadin duniyar nan suke ta karakaina tsakanin mulkin soji da na farar hula. Kowace Nahiya dai a yanzu ta kwalfi gardin dimokuradiyya, don haka take tsanar duk wani abin da ya shafi yunkuri na bakar aniyar masu amfani da kaki da kuma makamai wajen juyin mulki. Na yarda hakan, sai a gaskiya wannan malamin mai suna Bello Zubairu Idris bai zurfafa tunani ba. A ganina babu abin da ya hada rikicin Turkiyya da Nijeriya!

A ganina ya kamata dukkanin kafafen yada labarai musamman masu rajin kare hakkokin bil-adama su fito su nemi bahasin lamuran da ke faruwa a kasar ta Turkiyya, inda rahotanni ke bugun juna wajen nuna cewa ana ci gaba da kamawa tare da garkame wadanda ake tuhuma ba tare da mika su ga kotuna don fuskantar shari’u ba. Haka ma a daidai lokacin da ake tsaka da wannan kuma, kwatsam majalisar dokokin kasar Birtaniya ta fito da wata sanarwa inda ta kammala da cewa sam ko daya babu hannun Sheikh Gulen da magoya bayansa a cikin yunkurin na juyin mulkin da mahukunta kasar ke ta tayar da jijiyar wuya kan lamarin, kamar yadda kafar yada labarai na ‘Citi97.3fm’ ta bayyana. A cewar Wannan wata izina ce da ya kamata mahukuntan kasar su rika kalla don wanzar da zaman lafiya, fahimtar juna da ci gaban kasar.

Lokacin da yake mika rahoton, wani kwamiti a majalisar dokokin kasar ta Burtaniya ya ce, “Bayan kyakkyawan nasarin da muka gudanar dangane da yunkurin juyin mulki na kasar Turkiya da ya auku ranar 15 ga Yulin bara, musamman bisa la’akari da yadda aka dora karan-tsana a kan Gulen da mabiyansa, hakika babu wata kwakkwarar hujjar da za a iya fitowa da ita a kan bayyana su da hannu a cikin yunkurin na ranar 15 ga Yuli.”

Wannan makon dai yana cike da tarihi idan har aka lissafa kwanakin da rikicin ya dauka. Saboda haka tilas a dora alamun tambaya kan yadda ake kokarin sa idanu a kan ‘yan jarida da kuma wasu jami’ai.  Amma manazarta na ci gaba da dora manyan tambayoyi da har yanzu aka kasa fahimta, mene ne dalilin da ya sanya ake yakar bangare daya kawai? Me ya sa hukumomin kasar ta Turkiyya suka dora karar-tsana a kan fitaccen Malamin kasar, Fethullah Gulen? Wasu daga cikin rahotannin na cikin gida sun tabbatar da cewa rikicin tsakanin Shugaba Erdogan da Sheikh Gulen ba ya rasa nasaba da siyasa. A cewar rahotannin, Gulen yana daga cikin fitattun mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen ba wa Shugaba Erdogan goyon bayan samun shiga gidan sarautar kasar, amma daga bisani, wasu ‘yan ba-ni-na-iya suka shiga tsakani, wanda hakan ta tilasta wa Sheikh Fethullah barin kasar tasa ta gado, ya koma cikin kasar Amurka, inda a yanzu yake zaman gudun hijira.

Rahotanni daga wasu kafafen yada labaran kasashen Turai sun bayyana cewa shi dai Fethullah fitaccen malami ne da ya shafi shekaru da dama yana yin kira ga al’ummar Musulmi da su rika yin koyi da tafarkin rayuwar fiyayyen halittu Annabi Muhammad (SAW). Sakonnin yake aikawa a ko’ina a duniya shi ne, Musulmi shi ne kadai tsayayyen mutumin da zai iya tabbatar da zaman lafiya a doron kasa, ta hanyar ayyuka nagari. Sun kara da cewa a mafi yawan rubuce-rubucensa, Sheikh Gulen ya fi mayar da hankali kan yadda ake bata sunan addinin Musulunci musamman a yanzu da duniya ke kokarin danganta wasu gungiyoyin ta’addanci da Islam. A mafi yawan ra’ayoyin malamin, yana koyar da tsantsan zama a matsayin masu neman ilmi da aiki da shi. An dai ce malamin kusan ya fi kowa magoya baya daga ‘yan kasarsa, a ciki da wajen kasar ta Turkiyya, wanda a halin yanzu ya bude cibiyoyin koyar da ilmin addinin Islama a Nahiyoyi da dama, ciki, har da Afrika da mafi yawan kasashen na kasashen na Afrika, har ma da Nijeriya a ciki. Baya ga wannan ya kasance a kan gaba wajen yada manufar addini ta hanyar rubuce-rubucen littattafan da a yau ake fassara su zuwa yaruka sama da 60 na Afrika.

Ko a lokacin da al’amura ke ci gaba da ta’azzara, bayan dukkanin sakonnin nan da Sheikh Gulen yake aikewa zuwa ga mahukunta kasar tasa ta Turkiyya, sai ga shi a rana tsaka kallo ya nemi komawa sama, a lokacin da Shugaban Kasar Recep Erdogan ya bayyana Sheikh Gulen da cibiyarsa  ta ‘Hizmet’ a matsayin daya daga cikin wadanda suka shirya yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba. Jin haka, kamar yadda na karanta a wasu daga cikin manyan jaridun kasashen Turai da Amurka, Sheikh Gulen ya fito ya karyata zancen na Shugaba Erdogan. Kana kuma ya kara jaddada manufarsa, sannan ya nesanta kansa da cibiyarsa ta Hizmet daga abin da shugaban na Turkiyya ya bayyana.

Mafi mahimmancin abin da ya kamata al’umma ta fi mayar da hankali shi ne idan har irin haka na ci gaba da faruwa a kasar, wanda a yanzu dukkanin kungiyoyin da ke cikin kasar da ma na kasar waje suna ta kiraye-kiraye ga gwamnatin Erdogan da ta tashi haikan domin zakulo hakikan makiya muradun kasar, musamman wadanda suka nemi kassara ta, ta hanyar juyin mulki!

  • Rabi’u marubuci ne kuma dan jarida mai zaman kansa. Ya aiko wannan ne daga Abuja.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI